An bude sararin samaniyar Nijar bayan wata guda da juyin mulki
Sojojin sun bude sararin samaniyar wata guda bayan karbe iko da kasar.
Dakarun sojin Nijar sun bude sararin samaniyar kasar, wata daya bayan juyin mulkin da suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yuli.
Sojojin sun rufe sararin samaniyar kasar ne bayan da suka kwace mulki a ranar 26 ga watan Yuli, sai suka bude shi ranar 2 ga watan Agusta, sannan a ranar 6 ga Agustan kuma sai suka sake rufe shi bayan da kungiyar ECOWAS ta yi barazanar amfani da karfin soji don mayar da mulkin farar hula a kasar.
- Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan Zaben 2023
- Wasu ’yan siyasa na kokarin shirya wa gwamnatin Tinubu mummunar zanga-zanga – DSS
Mai magana da yawun ma’aikatar Sufurin Nijar, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran kasar (ANP), cewa bayan hakan an kuma dawo da sufurin motoci.
Sai dai duk da haka ba a bude harkar sufurin saman ga duk wasu ayyukan jiragen soji ba, ta yadda sai sun nemi izini daga hukumomin da suka kamata tukunna.
Yunkurin ECOWAS
A baya, Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka na Yamma (ECOWAS) ta kakaba wa Nijar takunkumai, bayan hambarar da Shugaba Bazoum, sannan ta yi barazanar amfani da karfin soji a matsayin mafita wajen warware matsalar idan har aka gaza sasantawa wajen mayar da mulki hannun farar hula.
A ranar 2 ga watan Agusta ne Nijar ta sake bude iyakokinta na kasa da kasashe biyar da suka hada da Aljeriya da Burkina Faso da Libya da Mali da kuma Chadi.
An bai wa wasu jiragen izini na musamman don ci gaba da aiki da filin jirgin sama na Yammai.
A ranar Juma’a ne Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa akwai dimbin kayan abinci da za a kai Nijar amma sun makale a hanya sakamakon rufe iyakokin kasar da sojoji suka yi.