An bude sashen noma don tallafa wa manona
Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha mallakar Gwamnatin Tarayya da ke Jihar Nassarawa, Dokta Shettima Abdulkadir Sa’idu, ya ce makarantar ta bude sasen koyar da ilimin harkokin noma don bunkasa harkar noma a jihar da kasa baki daya.Malamin wanda ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a ofishinsa da ke cikin makarantar, ya ce […]
Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha mallakar Gwamnatin Tarayya da ke Jihar Nassarawa, Dokta Shettima Abdulkadir Sa’idu, ya ce makarantar ta bude sasen koyar da ilimin harkokin noma don bunkasa harkar noma a jihar da kasa baki daya.
Malamin wanda ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a ofishinsa da ke cikin makarantar, ya ce sashen zai taimaka wa al’ummar jihar su cin ma burinsu na samar da abinci.
“A lokacin da muka shigo sai muka ga muna da sashen kimiyyar noma kuma da ma mun lura cewa al’ummar da ke Nassarawa manoma ne saboda haka sai muka bude sashen noma don mu tallafa wa al’ummar da ke tare da mu su cin ma burinsu na noma da kiwo.” Inji shi.
Ya ce sashen kari ne a kan sashen da makarantar take da shi na kimiyyar noma. Ya bayyana cewa sashen zai zama wata kafa da a nan gaba za ta ba da damar bude makarantar harkokin noma.
Shugaban ya bayyana cewa sun bude wasu sababbin sashen da suka hada da na kimiyyar jirgin kasa da sauransu don bunkasa ilimi da fannin kimiyya a tsakanin dalibai. Ya ce tuni hukumar makarantar ta tura wasu daga cikin ma’aikatan makarantar kasashen wajen don yin kwas da kara samun gogewa a kan fannonin kimiyya daban-daban.
Ya bayyana cewa a lokacin da ya karbi shugabancin makarantar, ya yi nazari sosai dangane da matsalolin da ke addabar makarantar. Inda a cewarsa sun lura makarantar babu isassun wuraren kwanan dalibai da ofisoshi da ajujuwa da dakunan kimiyya da fasaha.
Ya ce babban matakin da suka dauka shi ne na tunkarar matsalolin tare da magance su daki-daki. Ya bayyana cewa cikin shekaru biyu kacal sun yi ayyuka masu yawa a sashe-sashe da fannonin daban-daban na makarantar don bunkasa ilimin kimiyya da fasaha.