An bude tashar kashe gobara a kasuwar Potiskum

Shugaban Riko na karamar Hukumar Potiskum Alhaji Muhammad Musa Potiskum ya kaddamar da sabuwar tashar kashe gobara ta ‘yan kwana-kwana a karo na farko a babbar kasuwar Potiskum don rigakafin asarar dukiyoyi da ake samu idan gobara ta tashi a kasuwanni kafin kawo daukin jami’an kashe gobara.Da yake jawabi lokacin kaddamar da sabuwar tashar kwanakin […]

An bude tashar kashe gobara a kasuwar Potiskum
An bude tashar kashe gobara a kasuwar Potiskum

g Gwamnan Jihar Yobe Ibrahim GaidamShugaban Riko na karamar Hukumar Potiskum Alhaji Muhammad Musa Potiskum ya kaddamar da sabuwar tashar kashe gobara ta ‘yan kwana-kwana a karo na farko a babbar kasuwar Potiskum don rigakafin asarar dukiyoyi da ake samu idan gobara ta tashi a kasuwanni kafin kawo daukin jami’an kashe gobara.
Da yake jawabi lokacin kaddamar da sabuwar tashar kwanakin baya, shugaban ya ce ya yi hakan ne saboda irin yadda yake ganin yawaitar tashin gobara da ake samu a kasuwannin kasar nan wadda ya ce a yawancin lokaci rashin kai dauki da wuri kan kara yawaitar asarar da ake samu duk da cewa kaddara kan riga fata.
Alhaji Muhammad ya ci gaba da cewa wannan yunkuri nasa na samar da tashar kashe gobara bai kai ga nasara ba sai da ya samu amincewar gwamnatin jihar wadda ya ce ita ta sahale masa ya samu cimma wannan nasara.
Daga nan sai ya bukaci shugabannin ‘yan kasuwar Potiskum da su ba da cikakken goyon bayansu dangane da wannan yunkuri nasa musamman “ta wajen kaucewa aikata abubuwan da wani lokacin kan taimaka na haddasuwar gobara da kuma ba da gudummawarsu don ganin wannan tashar gobarar ta dore don kare rayuka da dukiyoyin jama’a a matsayin garin Potiskum shi ne cibiyar kasuwancin Jihar Yobe.
Har ila yau, ya kuma ba da tabbaci ga ‘yan kasuwan cewa, akwai yiwuwar nan gaba kadan idan dama ta samu a samar da karamin ofishin ‘yan sanda a harabar kasuwar don samar da cikakken tsaro, amma a cewarsa abubuwa da dama na ci gaban kasuwar ba za su yiwu ba har sai ya zamanto ‘yan kasuwar na hada kai da karamar hukumar wajen biyan kudin harajin kasuwar da suka san hakkinsu ne su bayar.
A karshe ya ce a yanzu haka yana da kudirin gina magudanun ruwa da tona rijiyoyin burtsatsai a wasu sassa na babbar kasuwar da kuma kasuwar hatsi da ta shanu don sake inganta harkokin kasuwancin karamar hukumar.