An bukaci a inganta hanyar Biu saboda Jami’ar Sojoji
Magatakardar Jami’ar Sojoji da ke garin Biu, Birgediya Janar Shu’abu Ibrahim ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gaggauta aikin hanyar Gombe zuwa Biu saboda Jami’ar Kimiyya ta Sojoji da ke garin Biu. Ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Biu, inda ya ce duk kusurwar […]
Birgediya-Janar Shu’abu Ibrahim, Magatakardar Jami’ar Sojoji ta Biu
Magatakardar Jami’ar Sojoji da ke garin Biu, Birgediya Janar Shu’abu Ibrahim ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gaggauta aikin hanyar Gombe zuwa Biu saboda Jami’ar Kimiyya ta Sojoji da ke garin Biu.
Ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Biu, inda ya ce duk kusurwar zuwa garin Biu daga ko’ina hanyar ba ta da kyau.
Ya ce Babban Hafsan Sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi kokari wajen kawo wannan jami’a garin Biu wacce babu irinta a duk Nahiyar Afirka, kuma Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta zo ta tantance kayayyakin aiki na jami’ar, amma sun koka da rashin kyan hanya.
“Ta dalilin kokarin Shugaban Sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai, kungiyoyi masu zaman kansu da masu hannu da shuni suna taimaka wa jami’ar ta hanyoyi daban-daban, domin yanzu kamfanin mai na Balami Oil ya tona rijiyar burtsatse da gina dakunan kwanan dalibai a jami’ar,” inji shi.
Ya ce jami’ar tana da fadin hekta dubu 500 kuma Gwamnatin Jihar Borno ce ta bayar game da wasu motoci don saukake wa dalibai zirga-zirga. Ya ce hanyoyin zuwa Biu ba su da kyau duk da kyan da jami’ar take da shi, wannan rashin kyaun hanya yana jawo musu cikas.
Don haka ya yi kira da babbar murya ga Gwamnatin Tarayya ta sa baki wajen ganin an fara aikin hanyar daga Gombe, tunda an bayar da kwangilar tun bara.
Shugaban Jami’ar Sojojin, Farfesa Dabid Iliya Malgwi, ya ce jami’ar ta fara ne tun a watan Afrilun shekarar 2018. Ya ce kasancewar jami’ar babu kamarta a Nahiyar Afirka, makin da suke karba na JAMB don shigar dalibai 180 ne babu canji.
Farfesa Malgwi ya ce yanzu haka sun rantsar da dalibai dubu daya da goma sha shida a zangon karatu na farko. Kuma ya bayyana cewa Kungiyar Injiniyoyi ta Kasa (NSE) tana gina Sashin Nazarin Injiniyanci a jami’ar, inda nan da wata biyu za a iya kammalawa.
Daga nan sai Shugaban Jami’ar ya ce yanzu jami’ar ta samu kason kudinta Naira biliyan biyu, wanda yanzu sun fara aikace-aikace da su, sannan sun samu tallafin kudi da za su gina hanyoyi a cikin jami’ar.