An bukaci a kawo karshen tallace-tallacen yara a Kebbi

An bayyana cewa tallace-tallace, musamman tsakanin kananan yara a Najeriya, musamman ta Arewa ya kasance tamkar wata al’ada, inda akan dora wa kananan yara abubuwan sayarwa kamar su goro, kosai, mangoro da dai sauransu. Kamar yadda Malam da M. Sule mai Shayi ya bayyana lokacin da Aminiya ke zantawa da shi, ya ce wannan dabi’ar […]

An bukaci a kawo karshen tallace-tallacen yara a Kebbi
An bukaci a kawo karshen tallace-tallacen yara a Kebbi

An bayyana cewa tallace-tallace, musamman tsakanin kananan yara a Najeriya, musamman ta Arewa ya kasance tamkar wata al’ada, inda akan dora wa kananan yara abubuwan sayarwa kamar su goro, kosai, mangoro da dai sauransu.

Kamar yadda Malam da M. Sule mai Shayi ya bayyana lokacin da Aminiya ke zantawa da shi, ya ce wannan dabi’ar ta tallace-tallace ta gurbata tarbiyyar yara kanana tare da sanya su a cikin wani halin da bai kamata su sami kansu ciki ba. Saboda haka ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kebbi da ta dauki matakan shawo kan matsalar, domin samun zuri’a tagari.
Kamar yadda bincikenmu ya nuna, wasu iyayen na tura yaransu talla, domin babu wata hanyar samun kudaden shiga amma wasu kuma sukan yi haka ne domin samun tazarar tara wa ’ya’yansu mata kayan aure idan lokaci ya yi. A jihar ta Kebbi, matsalar tallace-tallace ta fi kamari a yankunan karkara, inda yara kanana, musamman mata ke daukar kayan talla domin shigowa birane domin su saida.
Wannan dabi’ar ta jawo matsaloli da dama, musamman ta hanyar tarbiya da ma batun ilmi ga yara kanana, domin kashi tamanin na yaran da ke tallace-tallace ba su samun damar zuwa makaranta.
Kamar yadda wakilinmu ya gano, a garin Birnin Kebbi, wanda shine babban birnin Jihar Kebbi, akwai daruruwan yara, mata da maza a kan tituna suna talla kuma mafi yawancinsu sun zo ne daga kauyukan da ke kusa da garin, kamar Harasawa, Kardi, Zauro, Ambursa da Janzomo.