An bukaci a rika hukunta masu yi wa yara fyade
Shugaban Likitocin Babban Asibitin Jihar Jigawa, Dokta Abbas Ya’u Garba ya bukaci a rika hukunta masu yi wa yara fyade. Kuma ya ce fyade bai tsaya ga yara ba, ko matar mutum ne ya auka mata da karfin tsiya, ya yi amfani da ita ba da amincewarta ba, ya aikata fyade a dokar kasa da […]
Shugaban Likitocin Babban Asibitin Jihar Jigawa, Dokta Abbas Ya’u Garba ya bukaci a rika hukunta masu yi wa yara fyade. Kuma ya ce fyade bai tsaya ga yara ba, ko matar mutum ne ya auka mata da karfin tsiya, ya yi amfani da ita ba da amincewarta ba, ya aikata fyade a dokar kasa da aikin likita.
Shugaban ya bayyana haka ne a wajen wata bita da kungiyar yaki da cin zarafin mata da yara kanana ta shirya ga limaman masallatan Juma’a na Jihar Jigawa da nufin dakile yaduwar fyade da luwadi da suka addabi al’umma.
Ya ce wanda ya nuna wa matarsa karfi yayin jim’ai ba tare da amincewarta ba, idan ta yi kararsa a gaban kotu zai iya fuskantar hukunci.
Ya koka a kan yadda ba a yi wa wadanda suka aikata laifin luwadi da fyade hukunci, inda ya ce shi ne ke sa masu aikata laifin suke ci gab ada aikatawa.
“Fyade yana da illoli kamar sanya wa wadanda aka yi wa cutar kanjamau ko yoyon fitsari ga yara mata, yayin da yara maza da aka lalata ta hanyar luwadi suke samun matsalar rike ba-haya saboda lalata masu dubura da aka yi” inji shi.
Ya nuna takaicinsa game da yadda harkar luwadi ta yawaita a Jihar Jigawa, sabanin yadda a wasu jihohin ake lalata yara mata kanana. Ya ce bincike ne da masana suka yi ya tabbatar da haka a Enugu, kimanin wata uku da suka gabata.
Don haka ya shawarci iyayen da aka yi wa ’ya’yansu fyade ko luwadi su gaggauta kai yaran asibiti domin duba lafiyarsu saboda hukuma ta samu ikon ba su kariya.
Limamin Masallacin Juma’a na Kungiyar Izala da ke kan Hanyar Garun Malam, Muhammad Salihu Fagoji cewa ya yi harkar fyade da luwadi da ake yi da kananan yara ba wani abu ba ne da ya wuce tsafi. “Masu yi suna yi ne kawai domin son duniya amma babu wata maganar sha’awa a cikinsu. Masifa ce tunda dai masu yi suna yi da tsofaffi da kuma jarirai” inji shi.
Amma Limamin Masallacin Kwalejin Horon Malamai ta Gumel, Malam Haruna Hashim a nasa bayanin, cewa ya yi mafiya yawan wadanda suke aikata haka suna da ciwon hauka, saboda haka akwai bukatar a rika duba kwakwalwar wadanda aka samu sun aikata luwadi da fyade.
Shi kuma Liman Shu’aibu Usman takaicinsa ya nuna game da yadda ake ta kokarin dakile cutar amma abin ya ki ci ya ki cinyewa, sai karuwa yake yi kamar wutar daji. Ya ce matakin da kungiyar ta dauka na yin amfani da malamai wajen fadakar da al’umma a kan yaki da cin zarafin mata da yara kanana ya yi daidai.