An bukaci a yi wa Sarkin Musulmi biyayya a yankin Yarbawa

Shugabannin Musulmi a Kudu Maso Yamma sun nemi jama’a suyi aiki da umarnin Sarkin Musulmi bisa al’amuran da suka shafi ganin wata. Aare na Musulmin  kasar yarbawa da jihohin Edo da Delta Alhaji Daud Makanjuola ya yi kira ga al’ummar musulmi a wannan sashe da  suyi aiki da umarnin Sarkin Musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar wanda […]

An bukaci a yi wa Sarkin Musulmi biyayya a yankin Yarbawa

Daga Hagu Gwamnan Jihar Oyo, Seyi makinde tare da Aare na Musulmin kasar Yarbawa da jihohin Edo da Delta

Shugabannin Musulmi a Kudu Maso Yamma sun nemi jama’a suyi aiki da umarnin Sarkin Musulmi bisa al’amuran da suka shafi ganin wata.

Aare na Musulmin  kasar yarbawa da jihohin Edo da Delta Alhaji Daud Makanjuola ya yi kira ga al’ummar musulmi a wannan sashe da  suyi aiki da umarnin Sarkin Musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar wanda ya nemi al’ummar musulmi a Najeriya suyi Sallar Eidel-Fitr a cikin gidajensu domin gujewa cunkoson jama’a dake iya  haifar da yaduwar COVID-19 a cikin jama’a.

Alhaji Daud Makanjuola ya yi wannan kira ne a ranar Juma’a a  lokacin hirar sa da ‘yan jarida a Ibadan, inda  ya tunatar da al’ummar musulmi cewa wannan annoba ita ce tayi sanadin mutuwar mutane fiye da dubu 300 a duniya baki daya.

Yace Gwamnatocin kasashen duniya daban daban sun  kafa dokokin hana zirga zirga domin kariya daga wannan annoba, haka zalika  mahukumta a Najeriya ma sun kafa irin wadannan dokoki wanda ya zama wajibi ayi aiki da su domin gujewa yaduwar cutar.

Jagoran Musulmi na wannan yanki da aka fi sani da  Aare na  musulmi  ya nemi musulmin wannan sashe subi umarnin Sarkin Musulmi Sa’adu Abubakar wajen yin sallar idi a cikin gidajensu,  shi ma shugaban kungiyoyin Musulmi a jihar Oyo Alhaji Ishaq Kunle Sanni ya yi irin wannan kira ne a inda yace duka Al’ummar musulmi a wannan sashe suna jiran umarnin Sarkin Musulmi Sa’adu Abubakar ne a kan al’amuran da suka shafi addinin Islam.

Binciken da Aminiya ta gudanar a birnin Ibadan ya nuna cewa jama’a musulmi da kirista maza da mata suna can suna rububin shiga cikin kasuwanni domin sayan danyen kayan abinci abinci kamar shinkafa da wake da garin alubo da nau’in naman kaji da dabbobi domin gudanar da bukukuwan sallar idin bana.

A baya an saba ganin mabiya addinai suna taya ‘yan uwansu irin wadannan bukukuwan shekara shekara,yanzu haka birnin na Ibadan mafi girma a nahiyar Afrika ta yamma yana can cike da jama’a musamman irin wadanda suka dawo gida daga ciki da wajen Najeriya domin cakuda da ‘yan uwa wajen gudanar da bukukuwan sallar idin bana.