An bukaci al’ummar Arewa a Kudu da su hada kai
Sarkin Hausawan Ajeromi Ife lodun da ke Jihar Legas, Alhaji Adamu Abubakar Naby ya bayyana bukatar hadin kai a tsakanin shuwagabannin Hausawan jihar, domin a cewarsa a yanzu babu hadin kai kuma a saboda haka ne ’yan Arewa suka zamo koma baya a siyasar jihar duk da yawansu da ma gudunmawar da suke bayarwa a […]
Sarkin Hausawan Ajeromi Ife lodun da ke Jihar Legas, Alhaji Adamu Abubakar Naby ya bayyana bukatar hadin kai a tsakanin shuwagabannin Hausawan jihar, domin a cewarsa a yanzu babu hadin kai kuma a saboda haka ne ’yan Arewa suka zamo koma baya a siyasar jihar duk da yawansu da ma gudunmawar da suke bayarwa a siyasance a Legas.
“Rashin hadin kanmu ne ya sa masu kasar nan in za su yi wadansu mahimman abubuwa ba su sanya mu a ciki domin tuni suka ankara da bambance-bambancen da ke tsakaninmu. In ka duba al’ummar Ibo, shugaba daya ne da su, ba kamarmu Hausawa ba,” inji shi.
A cewarsa, dole ne al’ummar Hausawan da ke Legas su hada kansu, mutukar suna son ci gaba, domin a yanzu ko kwamishina ba a taba ba su ba amma su takwarorinsu Ibo sun sha samu ba iyaka, wanda hakan saboda amfanin hadin kan nasu ne ya jawo masu, kuma abin da ya janyo wannan bambance-bambancen shi ne a bangaren sarauta an rabu gida biyu. Haka ma a bangaren siyasa, to wannan inji basaraken, ita ce babbar matsalar. Domin haka ya yi kira ga sarakunan na Arewa da su sanya baki su zauna da shuwagabannin na ’yan Arewa mazauna Jihar Legas domin a yi sulhu, a samu matsaya, a fidda shugaba guda daya; a dinke barakar. In kuwa ba haka aka yi ba, to wannan gaba za a gadar wa jikoki da tattabakunne.