An bukaci cocin batican ta nemi gafara kan kisan kiyashin Ruwanda
A dai-dai lokacin da ake ci gaba da bikin cika shekaru 20 tun bayan kisan kiyashin da ya faru a kasar Rwanda, wata kotun musamman da Majalisar dinkin Duniya ta kafa don shari’ar wadanda ke da hannu a rikicin kasar ta samu cocin batican da hannu a kisan ‘yan kabilar Tutsi.Kotun ta gano cewa a […]
A dai-dai lokacin da ake ci gaba da bikin cika shekaru 20 tun bayan kisan kiyashin da ya faru a kasar Rwanda, wata kotun musamman da Majalisar dinkin Duniya ta kafa don shari’ar wadanda ke da hannu a rikicin kasar ta samu cocin batican da hannu a kisan ‘yan kabilar Tutsi.
Kotun ta gano cewa a lokacin kisan kiyashin wasu ‘yan kabilar Tutsi su 2000 sun shiga wata cocin Katolika don neman mafaka wanda wani Fada mai suna Wenceslas Munyeshyaka yake shugabanta. Fadan ya ba da umarnin murkushe su nan take, sakamakon wannan laifin ne kotun ta yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai. Amm wata kotun daukaka kara da ke kasar Faransa ta sallame shi cikin shekarar 2007. Bugu da kari kasar ta Faransa ta ci gaba da ba shi mafaka har zuwa yanzu.
Dangantaka tsakanin Faransa da Rwanda ta yi tsami ne bayan Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame ya zargi Faransar da hannu a kisan ‘yan kabilar Tutsi da kuma ‘yan hutu masu sassaucin ra’ayi a lokacin kisan kiyashin. Wannan ya sa kasar ta Rwanda ta hana Jakadan Faransa a kasar halartar bukukuwan cika shekaru 20 da aka gudanar don nuna alhini da kisan kiyashin.
A rawotan wata kungiya mai suna African Unity ta daura alhaki kan cocin Rwanda ne, sakamakon damar da take da ita a lokacin kisan kiyashin na hana yadowar rikicin kabilancin a kasar. Rawotan ya kara da cewa cocin ba ta yi amfani da damar ba, saboda yadda ta goyi bayan ‘yan kabilar Hutu. Don haka a cewar rawotan ya dace cocin Katolika da ke da hedkwata a batican da ta nemi gafarar jama’ar Rwanda. Kisan kiyashin dai ya faru ne kasar a cikin shekarar 1994 wanda ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane kimanin dubu 800.
A lokacin bikin cika shekaru 20 din, Shugaban kasar Paul Kagame ya kunna wata wuta da za ta kai kwanaki 100 tana ci, wanda aka tsara hakan don ya yi dai-dai da tsawon kwanakin da aka kwashe ana kisan kiyashin.
Har-ila yau, kisan kiyashin ya haifar da dubbannin ‘yan gudun hijira wanda har zuwa wannan lokaci akwai kimanin dubu 200 da ke zaune a Jamhuriyar Damukradiyyar Kongo.