An bukaci gwamnati ta bude babbar kasuwar Jos

Yan kasuwar da suke harkokin kasuwanci a babbar kasuwar Jos da aka rufe sakamakon tagwayen bama-baman da suka tashi a kasuwar a kwanakin baya, wanda ya yi sanadin asarar rayukan al’umma da dukiya, sun bukaci Gwamnatin Jihar Filato ta sake bude wannan kasuwa. ‘Yan kasuwar sun bukaci hakan ne a lokacin da suke zantawa da […]

An bukaci gwamnati ta bude babbar kasuwar Jos
An bukaci gwamnati ta bude babbar kasuwar Jos

Yan kasuwar da suke harkokin kasuwanci a babbar kasuwar Jos da aka rufe sakamakon tagwayen bama-baman da suka tashi a kasuwar a kwanakin baya, wanda ya yi sanadin asarar rayukan al’umma da dukiya, sun bukaci Gwamnatin Jihar Filato ta sake bude wannan kasuwa.
‘Yan kasuwar sun bukaci hakan ne a lokacin da suke zantawa da wakilin Aminiya a Jos shekaranjiya Laraba.
Shugaban ‘yan kasuwar Alhaji Abdurrahaman Jimo Yusuf  ya ce sun shiga cikin mawuyacin hali sakamakon wadannan tashin bama bamai, wanda ya yi sanadin asarar rayukan ‘yan kasuwar da dukiyoyi.
“A halin yanzu kuma mun kara shiga  cikin wani mawuyacin halin, sakamakon rufe wannan kasuwa musamman babban titin da  ya wuce ta gaban kasuwar. ‘Yan kasuwa na zaune ne ba sa yin komai, sakamakon rufe musu wannan waje da suke gudanar da harkokin kasuwancinsu.
Ya ce a yanzu ‘yan kasuwar sakamakon wannan hali da suka shiga da damansu ba su da kudin abinci.
“Don haka ina kira ga gwamnatin Jihar Filato da ta duba wannan hali da ‘yan kasuwar suka shiga, ta sake bude kasuwar da kuma titin da ya wuce ta gaban kasuwar.”
Ya ce: “Mun samu duk wadanda suka kamata mu samu kan wannan al’amari na rufe wannan kasuwa da wannan titi da yabi ta gaban kasuwar, amma suna cewa mu yi hakuri  maganar matsalar tsaro ce. Har yanzu dai muna kara tuna musu halin da muke ciki.”
Daga karshe ya bukaci ‘yan kasuwa su kara hakuri  kuma su ci gaba da yin addu’a har Allah Ya warware  wannan al’amari.