An bukaci gwamnati ta inganta noman doya
Dangane da korafe-korafen da jama’a ke yi na shugabanci game da kasuwar ’yan lemu ta Maraba da ke Jihar Nasarawa, masamman shiyyar ’yan doya, shugaban ’yan doya na kasuwar, Alhaji Abubakar Adamu wanda akafi sani Alhaji Uba Labour, ya ce duk filin kasuwar tasu da kudin gidauniya ne aka saye ta, inda kowanne dillalin da […]
Dangane da korafe-korafen da jama’a ke yi na shugabanci game da kasuwar ’yan lemu ta Maraba da ke Jihar Nasarawa, masamman shiyyar ’yan doya, shugaban ’yan doya na kasuwar, Alhaji Abubakar Adamu wanda akafi sani Alhaji Uba Labour, ya ce duk filin kasuwar tasu da kudin gidauniya ne aka saye ta, inda kowanne dillalin da ya sanya kudinsa a cikin gidauniyar ya samu shago ko rumfa, don haka ya yi kira ga gwamnati da ta inganta noman doya a jihar.
Shugaban ya ci gaba da cewa: “Muna da tsari na dillanci, lokacin gidauniyar sayen wannan fili, kowane dillali ya sanya kudinsa a ciki bayan mun sayi wadannan filaye sai muka fidda shaguna wadanda kowane dillali zai iya mallaka.”
Ya kuma nemi gwamnati da ta tallafa wa manoman doya ta yadda za a rika noma wadatatta kuma ana fitar da ita kasashen waje. A cewarsa: “Idan an lura, za a ga ana shigowa da kayan abinci daban-daban zuwa kasar nan, kamar su shinkafa, wake, tumatir da sauransu amma ban taba jin ana shigo da doya daga kasar waje ba. Don haka ya kamata gwamnati ta kirkiro da hayar fitar da doya kasar waje don samun kudin shiga a kasar nan baki daya. Ba zan mance ba, lokacin da na je Umura, na rike doya goma a kwali zuwa Saudiyya kuma na sayar da ita da matukar tsada, kusan ma in ce maka kudin Umurar sun kusa fotowa daga wannan doyar guda goma.”