An bukaci Gwamnatin Jihar Kaduna ta samar da Kekunan Napep
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadarru ta kasa (FRSC) na shiyar Saminaka da ke Jihar Kaduna, Mista J. S. Watu ya bukaci Gwamnatin Jihar Kaduna ta samar wa ‘Yan acaba Kekunan Napep don ceto su daga cikin mawuyacin halin da suka shiga. Kwamandan ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a […]
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadarru ta kasa (FRSC) na shiyar Saminaka da ke Jihar Kaduna, Mista J. S. Watu ya bukaci Gwamnatin Jihar Kaduna ta samar wa ‘Yan acaba Kekunan Napep don ceto su daga cikin mawuyacin halin da suka shiga.
Kwamandan ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a Saminaka Jihar Kaduna shekaranjiya Laraba.
Ya ce tun daga lokacin da dokar hana yin acaba ta fara aiki a Jihar Kaduna jama’a suka shiga cikin mawuyacin hali musamman masu wannan sana’a. Domin ta hanyar wannan sana’a ce suke ciyar da kansu da kuma iyalansu.
Ya ce saboda rashin kawo abubuwan hawan da za su maye gurbin baburan da aka hana yin haya da su ya sa mutane da dama suka shiga cikin tukura kan rashin abubuwan hawa don zuwa wuraren harkokinsu.
Ya ce ya kamata tun kafin a hana yin acaba gwamnati ta samar da Kekunan Napep kamar yadda wasu jihohi suka yi, domin kada jama’a su shiga cikin wani mawuyacin hali kan tafiye-tafiye.
Ya bukaci masu tuka taraktocin noma a yankin Saminaka su guji tukin ganganci kuma su sanya fitulu domin tafiyar dare da suke yi a wannan yanki.
“Wannan kiran ya zama wajibi musamman ganin a halin yanzu damina ta fadi, kuma a duk shekara a irin wannan lokaci direbobin taraktocin noma suka fi kawo hadurra sakamakon tukin ganganci da kuma tafiya babu fitila a yankin.” Inji shi.
Ya ce “Mun yi tarurruka da kungiyoyinsu kan wannan matsala, kuma mun ba su shawarar su gyara taraktocinsu, su kuma sanya fitilu tun da damina, sannan su guji tukin ganganci.”