An bukaci hadin kan Musulmi a ko’ina

An jadada bukatar da ke akwai ta limamai da kuma shugabannin addini su kara azama wajen hada kan al’ummar musulmi da kuma cigabansu ba tare da nuna wa juna kyara ko bambanci ba, musamman ta fuskar irin gudunmawar da kowane musulmi zai bayar wajen cigaban addinin.Wannan na cikin batutuwan da aka tattauna a wani taron […]

An bukaci hadin kan Musulmi a ko’ina
An bukaci hadin kan Musulmi a ko’ina

An jadada bukatar da ke akwai ta limamai da kuma shugabannin addini su kara azama wajen hada kan al’ummar musulmi da kuma cigabansu ba tare da nuna wa juna kyara ko bambanci ba, musamman ta fuskar irin gudunmawar da kowane musulmi zai bayar wajen cigaban addinin.
Wannan na cikin batutuwan da aka tattauna a wani taron da aka kira “Karin kumallo tare  da liman” kan bukatar hadin kai tsakanin musulmi, wanda aka gabatar a harabar makarantar islamiyya ta Darul Hidayatu Wal-Irshad da ke Kalaba, Jihar Kuros Riba.
A cikin wata mukala da shugaban makarantar, Malam Salim A. H. Tilde ya gabatar, ya bayyana muhimmancin hadin kai da tafiya tare tsakanin musulmi.
Shi ma a tasa kasidar, Alhaji Babatunde Abubakar Aliyu ya nuna bukatar a samar da wani dandali da sunan limamai da zai rika karade sauran limaman masallatai, ta yadda za a hadu a rika yin magana da yawu daya.
Ya ce lallai a sama wa ’ya’yan musulmi da ke karatun zamani a makarantu ’yanci,. wajen tuntubar shugabannin makarantun da nuna musu illar kiran ’ya’yan musulmi da sunan Boko Haram da ma  rika tilasta musu yin darasin addinin da ba nasu ba, sannnan da tattauna sauran wasu matsaloli da ka taso.
Haka nan an tabo illar sakaci wajen kin taimaka wa addinin da arzikin da Allah Ya huwace wa masu shi, wajen samar da gurbin aiki da sana’o’i ga daukacin matasa musulmi da kuma nuna kyamar juna da al’ummar musulmi kan yi tsakanin junansu, alhali a Musulunci babu magabar kabilanci.
Nuna bambancin kabila tsakanin musulmi ba alheri ba ne, domin akasarin wadanda suka karbi Musulunci, a wasu lokuta, ana yi musu cin fuska wajen kiran su sabbin tuba, alhali zamanin Manzon Allah, tsakanin Bilal da Balarabe an yi hanin da nuna wa mutum bambancin launin fata.
Taron ya yi tir da nuna halin ko-in-kula da wasu daga cikin musulmi da ke majalisun tarayya suke yi wajen tallafa wa da kuma hana yi wa Musulunci cin zarafi, idan bukatar haka ta taso.
Aminiya ta ji ta bakin Malama Asma’u  Nuhu Sani, daya daga cikin matan da suka gabatar da kasida kan kalubale da mata kan fuskanta a yankunan da ba musulmi ke da rinjaye ba, wajen gudanar da addini da kuma shiga irin wadda shari’a da tanadar wa musulmi.
Malama Asma’u  ta ce, “Babban kalubalen da ke gabanmu musulmi, musamman mata, shi ne karancin ilimin addini har ma da na zamani, wanda ke taimaka wa mace ta ba wa yaranta tarbiyya madaidaiciya. Wasu iyaye  na da sakaci wajen tarbiyyar yaransu, sai su ce nan ba Arewa muke ba, a kyale yaro ya rika yin abin da ya ga dama, kuskure ne, kuma lallai a daina nuna bambance-bambance tsakani”.
Ita ma Hajiya Hauwa’u  A. Ibrahim  ta yi tsokaci game da halin da musulmi suke ciki, musamman mazauna Kudanci, inda ta ce, “Ina jawo hankalin ’yan majalisun dokokinmu musulmi da su rika yin wani kazar-kazar na samar da wata doka da za ta hana ci wa musulmi fuska ko zarafi, musamman a Kudanci”.