An bukaci iyaye mata su lura da canjawar dabi’un ’ya’yansu

An bukaci iyaye mata su rika lura da dabi’un ’ya’yansu, don fahimtar canjawarsu.Alhaji Haruna Ibrahim Shugaban kungiyar Iyayen Yara da Malaman Makaranta (PTA) na Islamiyyar Darul Huda Wal Irshad da ke Kalaba, Jihar Kuros Riba ne ya bukaci hakan, a jawabin da ya gabatar wanda Sakataren kungiyar Musa Muhammad Kutama ya wakilta yayin walimar da […]

An bukaci iyaye mata su lura da canjawar dabi’un ’ya’yansu
An bukaci iyaye mata su lura da canjawar dabi’un ’ya’yansu

An bukaci iyaye mata su rika lura da dabi’un ’ya’yansu, don fahimtar canjawarsu.
Alhaji Haruna Ibrahim Shugaban kungiyar Iyayen Yara da Malaman Makaranta (PTA) na Islamiyyar Darul Huda Wal Irshad da ke Kalaba, Jihar Kuros Riba ne ya bukaci hakan, a jawabin da ya gabatar wanda Sakataren kungiyar Musa Muhammad Kutama ya wakilta yayin walimar da makarantar ta gudanar domin tafiya hutun azumi.
Shugaban ya tunatar da iyaye hakkin da ya rataya a wuyansu na tarbiyyantar da ’ya’yansu da kuma ba su ilmin addini da jaddada musu muhimmancin karatun alkur’ani mai tsarki.
Ya jawo aya ta shida da ke cikin suratul Tahrim inda Allah Madaukacin Sarki Ya gargadi wadanda suka yi imani da su tseratar da kansu da iyalinsu daga shiga wata wuta, wadda ake cika ta da mutane da kuma duwatsu.
“Idan iyaye suka ki karantar da iyalinsu, ko suka ki ba su tarbiyya, to hukunci mai tsanani zai hau kansu.” Inji shi.  
Alhaji Ibrahim Shugaban kungiyar Iyaye da Malaman Makarantar Islamiyyar Barikin Akim Kalaba ya ce, duk dan Adam makiyayi ne, za a tambaye shi dukkan abin da ya aikata.
Ya ce: “dan Adam mai kiwo ne, kuma abin tambaya ne, za a tambayi zama tsakanin mata da miji da da tsakaninsa da iyayensa, haka ma iyaye tsakanin su da ’ya’yansu.”
Assheik kazeem Lawal Abu Ridwanullah ya bukaci wadanda ba Musulmi ba su daina yi wa Musulmi kallon ’yan ta’adda.
Ya ce: “Musulunci na nufin zaman lafiya, ba ya koyar da ta’addanci ko tsageranci, wasu makiya Allah ne ke shafa wa addinin bakin fenti, amma da yardar Allah (SWT) ba za su ci nasara ba.
dalibai sun yi karance-karance, a karshe aka ba wadansu kyaututtuka.