An bukaci iyaye su kula da ’ya’yansu mata

Shugabar Kungiyar Mata Musulmi ta Kasa (FOMWAN), Hajiya Kulthum Abdullahi ta kirayi iyaye mata su sanya ido a kan ’ya’yansu mata kan su rika sanya hijabi domin kare martabarsu da kuma bin Sunnah. Shugabar ta bayyana haka ne a lokacin da take kaddamar da bikin Ranar Sanya Hijabi ta Duniya da aka gudanar a Jihar […]

An bukaci iyaye su kula da ’ya’yansu mata
An bukaci iyaye su kula da ’ya’yansu mata

Shugabar Kungiyar Mata Musulmi ta Kasa (FOMWAN), Hajiya Kulthum Abdullahi ta kirayi iyaye mata su sanya ido a kan ’ya’yansu mata kan su rika sanya hijabi domin kare martabarsu da kuma bin Sunnah.

Shugabar ta bayyana haka ne a lokacin da take kaddamar da bikin Ranar Sanya Hijabi ta Duniya da aka gudanar a Jihar Adamawa a farkon makon nan.

Ta ce ya kamata iyaye su dage wajen sanya wa yaransu mata kanana hijabi domin su saba da haha, ta yadda koda sun girma ba zai zame musu sabuwar al’ada ba.

Ta kara da cewa “Sanya hijabi ga mata a koyaushe na kare martabar kai  musamman a idanun al’umma.”

Ustaz Sa’id Abdulhamid ya gargadi iyaye mata wajen sanya wa ’ya’yansu hijabi da kuma nuna masu muhimmancinsa, domin kara daraja a tsakanin al’umma.