An bukaci iyaye su sa ido kan tarbiyyar  ‘ya’yansu

An jawo hankalin iyaye musamman mata su rika kulla alaka mai kyau da ’ya’yansu mata tare da zama da su don nuna musu abubuwan da suka shafi sirrin ’ya mace tun kafin ta san su a wajen kawayen da ba su dace ba. Wani malami mai suna Malam Isa Abbas ne ya yi wannan kira […]

An bukaci iyaye su sa ido kan tarbiyyar  ‘ya’yansu
An bukaci iyaye su sa ido kan tarbiyyar  ‘ya’yansu

An jawo hankalin iyaye musamman mata su rika kulla alaka mai kyau da ’ya’yansu mata tare da zama da su don nuna musu abubuwan da suka shafi sirrin ’ya mace tun kafin ta san su a wajen kawayen da ba su dace ba.

Wani malami mai suna Malam Isa Abbas ne ya yi wannan kira a lokacin taron kaddamar da wani littafi kan tarbiyyar matasa mai suna Kukan Kurciya da wani matashi ya rubuta, wanda aka gudanar a dakin taro na Women Center da ke garin Kafanchan ranar Asabar da ta gabata.

Malam Isa Abbas, wanda ya yi jawabi kan gudunmawar iyaye ga tarbiyyar al’umma, ya ce wajibi ne iyaye su tashi tsaye wajen kula da shige da ficen ’ya’yansu saboda halin da ake ciki na yaduwar fasadi a cikin al’umma.

“Iyaye za su sauke nauyin da ke kansu ne ta hanyar fara cusa wa ’ya’yansu tsoron Allah a dukkan lamuransu tare da koya musu kunya da amana da gaskiya a rayuwarsu,” inji shi.

Lokacin da yake yi wa Aminiya karin haske, mawallafin littafin, Abubakar Inuwa Idris ya ce babban makasudin rubuta littafin shi ne ganin yadda ayyukan assha suka yi yawa a cikin al’umma kuma akasari matasa ne suke shafa, don haka ya ga ya kamata ya bayar da tasa gudunmawar ta hanyar fito da dan karamin littafin da zai taimaka wajen fadakar da matasan.

“Babban abin takaici za ka ga hatta a masallatai sai an yi wa agogo gidan karfe an saka kwado an kulle saboda gudun kada a sace,” inji shi

Ya yi kira ga matasa su yi amfani da kuruciyarsu wajen kusantar Allah da samar wa kansu da al’ummarsu makoma tagari da a a yi alfahari da su nan gaba.

Mawallafin ya taba wallafa wani littafi mai suna Makomar Jihar Bauchi, inda ya ce akwai wasu littattafai biyu da yake shirin fitarwa nan gaba masu suna; Nasiha ga Masu Mulki da kuma, Jinya da Mutuwa.

Babban mai kaddamar da littafin, Lifidin Jama’a Alhaji Bashir Idris ta hannun wakilinsa ya sayi kwafi uku na littafin a kan Naira dubu 20  kuma ya bada kudi nan take kafin sauran jama’a suka ci gaba da saye.