An bukaci kasashen duniya su ja damara wajen yaki da fataucin miyagun kwayoyi
An bukaci hukumomin duniya da su mike tsaye domin yaki da fatauci da kuma shan miyagun kwayoyi, wanda yake wa jama’a da yawa illa. Shugaban kula da fatauci miyagun kwayoyi na Majalisar dinkin Duniya, Mista Yury Fedetob ne tare da tsohon shugaba Cif Olusegun Obasanjo, wanda yanzu shi ne shugaban hukumar yaki da fataucin miyagun […]
An bukaci hukumomin duniya da su mike tsaye domin yaki da fatauci da kuma shan miyagun kwayoyi, wanda yake wa jama’a da yawa illa.
Shugaban kula da fatauci miyagun kwayoyi na Majalisar dinkin Duniya, Mista Yury Fedetob ne tare da tsohon shugaba Cif Olusegun Obasanjo, wanda yanzu shi ne shugaban hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi na kasashen Afirka ta Yamma da shugaban hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi na Najeriya suka ba da wannan sanarwar bukata.
Shugabannin suka ce ba kasashen Afirka ne kadai ke fama da wannan kalubalen ba, a’a, kusan duk kasashen duniya ne, sai dai wata kasa ta fi wata kwazo da kuma doka mai tsanani game da wannan mummunar dabi’ar. Saboda haka suka ce kowa na da tasa gudummawar da zai bayar wajen ganin an fatattaki wannan annoba.
Suka ce wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa da yawan kasashen duniya suke fama da aikata manya-manya ayyukan assha, tare da fuskantar kalubalen tabarbarewan tsaro, wanda haka yana nufin koma baya ga duk wata al’ummar da ta samu kanta cikin wannan yanayi. “Kuma kowace kasa ta duniya tana da karfi bakin gwargwadon hali na yadda za ta fuskanci wannan matsalar, sai dai kila rashin shugabannin da suka mayar da hankalin a kan illar wannan lamari take hana su tabuka komai”. Inji su.
Wadannan shugabannin suna magana ne a taro karo na 57 da aka yi a biana a kan yaki da sha tare da fataucin miyagun kwayoyi na duniya.
Sa’ilin da yake jawabinsa wajen taron, shugaban hukumar NDLEA, Alhaji Amadu Giade ya ce duk da yake Najeriya na bakin kokarinta, amma rashin wadattaun kudin tafiyar da hukumar ya zame karfen kafa, wanda da tuni kasar ta tsufa da fatattakar dillalan kwayoyi a cikinta.
Shi ko Mista Fedotob cewa ya yi fatarsa ya ga cewa kasashen duniya sun baiwa samar da kwayoyi ko kuma magunguna nagari fifiko, wanda zai maye gurbin masu amfani da miyagun kwayoyi a matsayin abin biyan bukatarsu. Shi kuma tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, a nasa jawabin cewa ya yi yana fatar ganin an shawo kan hana masu hambudar miyagun kwayoyi ta hanyoyi daban-daban, domin ta haka ne ake kara samun yawaita ayyukan assha cikin al’umma.
Kusan duk wanda ya yi jawabi a wajen wannan taron, ba wanda bai tabo bukatar kara wa masu wannan aikin yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi kudin da za su iya aiwatar da wannan gagarumin aiki, wanda duk dan kasa nagari na da gudunmawar da zai ba da ta wannan fannin.
Daga karshe suka ce akwai bukatar samar wa matasa aikin yi, musamman a kasashen Afirka domin kawar da hankulansu daga harkokin shan miyagun kwayoyi.