An bukaci majalisa ta yi dokar tilasta wa ma’aikatan gwamnati kara aure
An sanya sharadin cewa sai ma’aikatan sun kara aure za su samu karin girma a ofis.
Wani shehin malamin addinin Islama, Sheikh Aminu Baba Waziri, ya yi kira ga ‘yan majalisa da su kafa dokar da za ta tilasta wa ma’aikatan gwamnati da suka kai mataki na 12 su kara aure.
Ya yi wannan kiran ne a wata huduba da ya yi a Babban Masallacin Takur da ke Dutse a Jihar Jigawa.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa, sun kashe mutane da dama a ƙauyen Kano
- Yadda farashin kayayyaki ya yi tashi mafi girma cikin shekaru 20 a Najeriya
Ya ce idan aka yi la’akari da yawan matan da ake da su a cikin al’umma, akwai bukatar maza su duba yiwuwar da kara auro wasu mata domin ci gaban al’umma.
Sheikh Waziri ya bayyana damuwa kan yadda duk cewa da akwai tarin mata zawarawa da wadanda ba su taba yin aure bakuma suna son yin auren, amma maza musamman wadanda suka yi aure ba sa kara mata.
Ya bayyana cewa, ana daukar aure a matsayin daya daga cikin muhimman ginshikai a Musulunci, wanda babu shakka Alkur’ani da Sunnar Annabi Muhammad (SAW) suna jaddada muhimmancinsa da kimarsa a wurin Allah.
Ya kafa hujja da aya ta hudu ta suratul Nisa’i da ke cikin Alkur’ani mai girma wadda Allah yake cewa ; “Kuna tsoron kada ku yi adalci ga marayu, ku auri wadanda kuke so, biyu ko uku ko hudu, amma idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci a tsakaninsu ba, sai ku auri guda daya, ko abin da hannayenku na dama suka mallaka, wannan shi ne mafi dacewa domin tseratar da kanku daga zalunci.”
Malamin ya bukaci ‘yan majalisar su zartar da dokar da za ta tilasta wa ma’aikatan gwamnati da ke mataki na 12 masu mata daya kacal su kara wata a matsayin sharadin samun karin girma a ofis.