An bukaci malamai su guji wa’azin tunzura mutane

Babban Sakataren Hukumar Kula da Harkokin Addinin Musulunci ta Jihar Kaduna, Alhaji Abdulrahman Mahmoud ya shawarci malaman addinin Musulunci su guji yin wa’azin da ka iya tunzura mutane, musamman matasa su ta da rikici.Alhaji Abdurrahman Mahmoud ya ce abu ne mai hadari malami ya rika yin wa’azi a masallaci ko wani wuri da zai iya […]

An bukaci malamai su guji wa’azin tunzura mutane
An bukaci malamai su guji wa’azin tunzura mutane

Babban Sakataren Hukumar Kula da Harkokin Addinin Musulunci ta Jihar Kaduna, Alhaji Abdulrahman Mahmoud ya shawarci malaman addinin Musulunci su guji yin wa’azin da ka iya tunzura mutane, musamman matasa su ta da rikici.
Alhaji Abdurrahman Mahmoud ya ce abu ne mai hadari malami ya rika yin wa’azi a masallaci ko wani wuri da zai iya tunzura mutane su yi rigima, inda ya ce hakan abu ne da ya saba wa karantarwar addini.
Babban Sakataren ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga wasu malamai da limaman daga garin Jere a karamar Hukumar Kagargo da suka kai masa ziyara a ofishinsa a makon jiya.
Alhaji Abdulrahman ya ce dole ne a yi duk abin da ya kamata domin kauce wa irin rikicin da ya faru a bayan zaben shekarar 2011. “Mun san abin da ya faru a shekarar  2011 a jihar nan. Saboda haka dole ne mu yi kokari wajen ganin hakan bai sake faruwa ba nan gaba. Musamman yanzu da zaben shekarar 2015 ke tunkaro mu. Hakkin malamai ne su fada wa mutane gaskiya sannan a kuma san abin da za a fada wa mutane da zai samar da zaman lafiya,” inji shi.
Ya ce babu wata jam’iyyar siyasa a kasar nan da za a ce ita ce ta Musulmi ko ta wadanda ba Musulmi ba.
Sai ya tabbatar wa bakin nasa cewa a shirye gwamnatin jihar take wajen ci gaba da taimaka masu kamar yadda ta taimaka wa masallatai da coci-coci kwanan nan.
Da yake jawabi tun farko, shugaban ayarin Malam Tahir Ibrahim Jere cewa ya yi sun kai ziyarar ce domin nuna godiyarsu ga gwamnatin jihar bisa taimakon kudi da ta ba makarantu da masallatai da su ma suka amfana.
Ya tabbatar wa Gwamnan Jihar, Muktar Ramalan Yero cikakken goyon bayansu wajen ganin an samu tabbataccen zaman lafiya a jihar baki daya.
Mai ba Gwamnan Jihar Shawara kan Harkokin Aikin Hajji, Alhaji Hassan Jere ya bukaci a cigaba da yin addu’o’i domin Allah Ya kawo karshen masu satar shanu a yankin Jere da kuma jihar.