An bukaci manoman shinkafa a Jihar Kaduna su biya rancen da gwamnati ta ba su
Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) reshen Jihar Kaduna, Alhaji Mohammed Numbu, ya yi kira ga manoman da suka amfana da rancen noman shinkafa a bara su gaggauta biyan rancen musamman wadanda suka fito daga Shiyya ta Uku (Kudancin Kaduna). Shugaban, ya yi wannan kira ne, yayin ganawa da shugabannin kungiyar manoman shinkafa na […]
Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) reshen Jihar Kaduna, Alhaji Mohammed Numbu, ya yi kira ga manoman da suka amfana da rancen noman shinkafa a bara su gaggauta biyan rancen musamman wadanda suka fito daga Shiyya ta Uku (Kudancin Kaduna).
Shugaban, ya yi wannan kira ne, yayin ganawa da shugabannin kungiyar manoman shinkafa na kananan hukumomi takwas da ke Kudancin Kaduna da aka gudanar a garin Kafanchan, inda ya ce gaggauta biyan rancen shi zai sake bai wa manoma damar sa ke cin wata gajiyar, ciki har da sababbin manoman da ba su samu a wancan karo ba.
Alhaji Mohammed Numbu, ya bayyana taron a matsayin wata hanya ta sake tsarawa tare da fito da wasu hanyoyin amso rancen saboda manoman sun riga sun yi girbi.
Shugaban, wanda ya bayyana takaicinsa kan matsalolin da aka ci karo da su a bara da suka hada da ambaliya da zuwan kakar zabe sun kawo cikas ga maido da rancen, ya nuna a bana lamarin ba haka yake ba, inda ya yi kira ga manoman su bayar da hadin kai wajen maido da rancen don shirin ya yi nasara.
A jawabin Manajan Bankin Unity reshen Kafanchan, Mista Marshal Kogi Karo, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan taimaka wa manoma da ta yi wajen ba su rance don bunkasa harkokinsu, inda ya yi kira ga manoman su tabbatar sun biya rancen da ke kansu.