An bukaci masu yabon Annabi su kyautata kalmomin wakokinsu
Wani malamin addinin Musulunci a Kano, Barista Habibu dan Almajiri, ya yi kira ga masu wakokin yabon Manzon Allah (SAW) su rika sanin irin kalmomin da suke amfani da su, domin a cewarsa, ba kowace irin kalma ake gaya wa Manzon Allah ba.Malamin ya yi wannan kira ne a yayin amsa tambayoyi a gidan Rediyon […]
Wani malamin addinin Musulunci a Kano, Barista Habibu dan Almajiri, ya yi kira ga masu wakokin yabon Manzon Allah (SAW) su rika sanin irin kalmomin da suke amfani da su, domin a cewarsa, ba kowace irin kalma ake gaya wa Manzon Allah ba.
Malamin ya yi wannan kira ne a yayin amsa tambayoyi a gidan Rediyon Edpress FM da ke Kano. Ya ce Allah Ya nuna wa Musulmi yadda za su kula yayin fadin wani zance da ya shafi Manzon Allah.
Ya ce dole ne duk mai yabon Annabi ya kasance kusa da malamai, domin su rika duba masa kalmomin wakarsa, su tabbatar da cewa babu kalma guda wacce ba ta dace a fade ta ga Manzon Allah ba. “Kada mai yabo ya ce wakarsa daga kansa sai sutudiyo kai-tsaye, dole ya kai ta wurin malami ya duba ya ga ko kalmomin sun dace a fade su a kan Manzon Allah (SAW).
Malamin ya kara da cewa yin haka wajibi ne domin kada garin yabo, mawakin ya je ya aikata sabo. Ya ce kwatankwacin kyawun abin da mawaki ya fada, kwatankwaci yadda za a saka masa. “Ya kamata mai yabon Annabi ya san cewa duk abin da ya fada ana kai shi gaban Annabi, a ce ga wane dan wane ya yabe ka.”