An bukaci mutane su koma ga Allah
An bayyana cewa karatun Alkur’ani shi ne madogara ga dukkan Musulmi kuma duk wanda Allah Ya hore wa sanin littafin Allah shi ne dan birni, domin duk wanda Allah Ya hore wa ilimin Alkur’ani ba bakauye ba ne.Hakan ya fito ne daga bakin Malam Inuwa Muhammad Ali, a wajen musabakar Alkur’ani ta bana da aka […]
An bayyana cewa karatun Alkur’ani shi ne madogara ga dukkan Musulmi kuma duk wanda Allah Ya hore wa sanin littafin Allah shi ne dan birni, domin duk wanda Allah Ya hore wa ilimin Alkur’ani ba bakauye ba ne.
Hakan ya fito ne daga bakin Malam Inuwa Muhammad Ali, a wajen musabakar Alkur’ani ta bana da aka gudanar a garin Dutse, Jihar Jigawa Ya kara da cewa, littafin Allah shi ne madogara kuma sh ine mafita ga dukkan Musulmi, duk wanda ya bi shi ya tsira.
Shi kuma Dokta Aliyu Haruna na Jami’ar Bayaro Kano, a nasa jawabin, ya kara da cewa mafiya shahara a malaman kasar Hausa ’yan Jihar Jigawa da suka tafi wasu jihohin da ma sauran kasashen Afirka suka yi fice, su ne ake alfahari da su a halin yanzu a fadin duniya.
Ya kuma shawarci jama’a da su koma kan gaskiya, su bi hanyar daidai, domin jama’a sun bar Allah shi ne ya sa Allah Yake jarrabarmu da iftila’i kala-kala. Ya koka game da irin dimbin matsaloli da kasar nan take fama da su, wadanda suka hada da rashin tsaro da annoba, wadanda ya ce kuma duk suna faruwa ne sakamakon barin Allah da Jama’a suka yi. Don haka ya shawarci jama’a su koma ga bin tafarkin Allah
Malamai irin su Abdullahi Gero, su ma sun samu damar tofa albarkacin bakinsu. Sun yi mamakin yadda gwamnatin jihar da sarakuna da sauran masu fada a ji wajen harkar addini suka zage damtse wajen taimaka wa harkokin addini, musamman wajen Musabaka ta bana.
A yayin rufe gasar, Ustaz Abbas Yakubu Abbas na hukumar addini ta Jihar Jigawa, ya yaba wa gwamnatin jihar da kuma gode wa duk wadanda suka bayar da gudunmawarsu wajen ganin musabakar ta yi nasara. Ya kuma hori zakarun musabakar na bana a jihar, da su yi kwazo wajan ciwo wa jihar kambun nasara, a gasar da za a yi a Jihar Nasarawa, a watan gobe.