An bukaci Naira miliyan 50 don sakin mahaifiyar ma’aikacin Gwamnan Jigawa
Masu garkuwa da mutane shida da suka shiga gidan mahaifiyar Yahaya Mohammed tsohon mai bai wa Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, shawara akan harkokin siyasa, sun bukaci a biya kudin fansa kafin a sako wanda suka yi garkuwan da ita. An dai yi garkuwan da mahaifiyar Yahaya, mai suna Hajiya Ladi mai shekaru 70 a […]
Masu garkuwa da mutane shida da suka shiga gidan mahaifiyar Yahaya Mohammed tsohon mai bai wa Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, shawara akan harkokin siyasa, sun bukaci a biya kudin fansa kafin a sako wanda suka yi garkuwan da ita.
An dai yi garkuwan da mahaifiyar Yahaya, mai suna Hajiya Ladi mai shekaru 70 a gidanta da ke kauyen Kaya a garin Suletankarkar jihar Jigawa ranar Talata.
Wani da yaso a sakaya sunansa ya ce, a yanzu haka suna kci gaba da tattaunawa da masu garkuwan da sasantawa yadda za a sako ta.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa Bala Zama Sanchi, ya tabbatar da aukuwar hakan ya ce a yanzu haka suna kokarin yadda za a sako Hajiya Ladi.