An bukaci sabon Shugaban kasa ya kafa kwamitin kula da marayu

An bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kafa kwamitin kula da inganta rayuwar marayu, wadanda aka kashe masu iyayensu a hare-haren da kungiyar Boko Haram suka kai wa jama’ar yankin Arewa maso gabas da wasu matan da kuma aka mayar da su zawarawa. Yusuf Habibu Turtsawa, wani dan siyasa mazaunin Layin Bagobiri, Unguwar Hausawa […]

An bukaci sabon Shugaban kasa ya kafa kwamitin kula da marayu
An bukaci sabon Shugaban kasa ya kafa kwamitin kula da marayu

An bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kafa kwamitin kula da inganta rayuwar marayu, wadanda aka kashe masu iyayensu a hare-haren da kungiyar Boko Haram suka kai wa jama’ar yankin Arewa maso gabas da wasu matan da kuma aka mayar da su zawarawa.

Yusuf Habibu Turtsawa, wani dan siyasa mazaunin Layin Bagobiri, Unguwar Hausawa da ke garin Kalaba Jihar Kurosriba ne ya bukaci haka, a zantawarsu da Aminiya. Ya ce: “Lura da irin barna da asarar rayukan bayin Allah Musulmi da Kirista da aka yi, musammman shiyyar Arewa maso gabas babban kalubale ne ga wannan gwamnati wajen kafa kwamitoci da za su lura da yadda za a farfado da inganta rayuwar mutanen da rikicin Boko Haram ya ya daidaita, da yake rikicin ya shafi dukkan mabiya addinan biyu, wajen kafa masu cibiyoyin koyon sana’o’i da kuma ayyukan hannu; ta yadda za su rage dogara da tallafin da gwamnati ke ba su ko a kowane sansanin ’yan gudun hijira.”
dan siyasar ya ci gaba da cewa: “Ina tunatar da Shugaban kasa da cewa, duniya fa yanzu ta zura masa ido don gyara kwamacalar da gwamnatin baya ta yi wa al’umma da kuma tattalin arzikin kasa. Ta kowace fuska an samu tawaya, al’umma sun maka zuru domin su ga gyaran da za ka yi wa kasa da al’ummarta, domin gida da waje an yanke kauna da gwamnatin da ta bar mulki wajen sukurkucewar tattalin arziki da kuma na tsaro”
Ya nemi ilahirin ’yan Najeriya da su dukufa wajen taya Shugaban kasa da kuma sauran zababbun ’yan majalisar tarayya da na jihohi addu’ar Allah Ya ba su ikon rike amanar da aka dora musu, Ya ba su damar gudanar da adalci da mulki na gaskiya. A cewarsa, addu’a ce ta dace a rika yi wa shugabanni, ba la’antar su ba. Ya kara da cewa kwarjini da martabar da Muhammadu Buhari ke da su a idon duniya na kara sanya masu kwarin gwiwar ceto halin da sugabannin baya na siyasa suka jefa ta a ciki.
Daga karshe dan siyasar ya jaddada bukatarsa ga kowane dan Najeriya da ya zage damtse ya ba kasar nan da shugabanninta tasa gudunmawar, ba su jira abin da gwamnati za ta yi masu ba.