An bukaci Sanata ta fice daga zauren majalisa saboda jinin al’ada
Abin takaici an kore ni ne saboda ina jinin haila.
An bukaci ficewar wata ‘yar Majalisar Dattawan kasar Kenya daga majalisar bayan halartar wani zama saboda tana jinin al’ada.
RFI ya ruwaito cewa ta halarci zaman ne tana sanye da farin kaya mai dauke da ratsin ja a wani gangamin wayar da kai game da jinin al’ada.
- Kotu ta tura ’yan TikTok gidan yari a Kano
- Zulum ya bai wa asibitocin gwamnati umarnin bayar da magani kyauta
Gloria Orwoba, ’yar jam’iyyar da ke mulki, za ta gabatar da wani kudiri kan samar da audugar mata kyauta, a wani bangare na kawo karshen jin kunyar da mata ke fuskanta a lokacin da suke jinin al’ada.
Rahotanni sun bayyana cewa, Sanatoci sun hargitsa zaman da aka yi da yammacin ranar Talata domin jawo hankalin Shugaban Majalisar kan shigar da ba su dace ba na Misis Orwoba.
Amma Sanatar ta nuna rashin amincewarta tana mai cewa: “Na yi mamakin yadda wani zai iya tsayawa a nan ya ce an wulakanta majalisar saboda mace ta yi al’ada.”
Kakakin Majalisar, Amason Kingi, ya umarci Sanatar da ta je ta sauya kayan da ke jikinta kafin a bata damar sake shiga zauren majalisar.
A wajen majalisar, Sanata Orwoba ta tabbatar wa manema labarai cewa, “Abin takaici an kore ni ne saboda ina jinin haila.
“Kuma bai kamata mu nuna hailar ba a lokacin da muke al’adar ba, kuma irin wannan shi ne cin mutuncin ’ya’ya mata.”