An bukaci ’yan Adawa su kara hakuri

Wani dan siyasa a Kudu ya shawarci kungiyoyin da ke adawa da gwamnati da su yi hakuri su bar gwamnati ta yi aikinta yadda ya dace. Ya ce kafa kungiyoyi da nufin dakushe kaifin jam’iyyar APC kasar nan tamkar ihunka banza ne, domin na gaba ai ya riga ya yi gaba, babu wata kungiya da […]

An bukaci ’yan Adawa su kara hakuri

Wani dan siyasa a Kudu ya shawarci kungiyoyin da ke adawa da gwamnati da su yi hakuri su bar gwamnati ta yi aikinta yadda ya dace. Ya ce kafa kungiyoyi da nufin dakushe kaifin jam’iyyar APC kasar nan tamkar ihunka banza ne, domin na gaba ai ya riga ya yi gaba, babu wata kungiya da wani ko wasu za su kafa ta zama barazana ga jam’iyyar APC kasar nan.

Umar Idris dan Walawa ne ya furta haka a zantawarsa da Aminiya. Ya ce “samun ci gaban da aka yi a kasar nan musamman mulkin wannan gwamnati ba abin da za a kwatanta da shi ba ne kana kuma zaman lafiya da mutunta juna kadai da aka samu tsakanin ’yan Najeriya ya isa babbar riba, musamman irin tasku da mulkin jam’iyyar adawa PDP ta yi ya jefa mutane cikin matsala, tsawon shekara 16 da suka yi suna mulkin kasar nan.”

dan siyasar ya ci gaba da cewa a wancan lokaci rayuwa ba ta ingantuwa, mabiya addinan nan biyu kowa na shakkar kowa, babu yarda da juna bare ma’amala kyakkyawa a tsakani; domin duk abinda aka ce babu zaman lafiya to ba za a samu ci gaba ba.

“Alhamdu lillahi, a mulkin Baba Buhari an samu zaman lafiya, su kuma wadanda ba su son zaman lafiya abin da suke bakin ciki ke nan, shi ya sa suke murna da rikicin Fulani makiyaya da manoma da rikicin kabilanci a wasu sassan kasar nan. Wannan duk ba wani abu ba ne face siyasa da kuma son a bata wannan gwamnati to amma duk mai hankali da son zaman lafiya ya marasa kishin kasar nan ne suke haddasa shi,” inji shi.