An bukaci ’yan Arewa su rike katin shaida a Jihar Ondo
Sabon Sarkin Hausawan Kasuwar Shasha, a garin Akure, hedkwatar Jihar Ondo, Alhaji Shehu dan Gari ya yi na’am da shirin tantance masu shiga cikin jihar daga Arewa. “Mun goyi bayan wannan mataki domin tabbatar da tsaro da bin doka da oda”. Inji shi, jim kadan bayan wani zaman tattaunawa da ’yan majalisarsa a kan wannan […]

Sabon Sarkin Hausawan Kasuwar Shasha, a garin Akure, hedkwatar Jihar Ondo, Alhaji Shehu dan Gari ya yi na’am da shirin tantance masu shiga cikin jihar daga Arewa.
“Mun goyi bayan wannan mataki domin tabbatar da tsaro da bin doka da oda”. Inji shi, jim kadan bayan wani zaman tattaunawa da ’yan majalisarsa a kan wannan batu a Akure, a wata hira da wakilinmu.
Alhaji Shehu ya ce irin katin da ake bukata ya hada da katin dan kasa ko na sanannun kungiyoyi ko takardar shaidar haihuwa ko kuma rubutacciyar wasika daga sanannen mutum ko kungiya daga gari kaza zuwa gari kaza.
“Yin haka yana da muhimmanci saboda kyautata tsaron lafiyar kasa kuma, har ma mun fara daukar matakan wayar da kan mutanenmu ta kafofin labarai da masallatai da kasuwanni da tasoshi da sauran wuraren taruwar jama’a. Za mu kafa wani kwamiti da zai rinka zagayawa domin fadakar da mutanenmu dangane da wannan al’amari.” Inji shi.
ya yi nunin cewa mutanensa da suke jihar an fara ba su takarda mai dauke da sunansa da hatiminsa da sa hannunsa, wanda ke zame musu a matsayin shaida.
Dangane da wadanda ba su da irin wadannan kati da takardun shaida, mahukunta za su yi musu binciken kwakwaf tare da tsare shi har sai sun gamsu da sahihancinsa.
A karshe ya yi kira kira ga kungiyoyin masu motocin sufuri na Arewa da ’yan kamasho su daina amincewa da lodin kaya da dimbin mutane a cikin mota daya, saboda matakin da aka ce za a dauka kansu. Ya bukaci ’yan kamasho su yi adalci da tare da tausaya wa ’yan uwansu, musamman saboda gudun hadari, wanda kan ci mutane masu yawa, idan ya auku. “Ina ganin ba sai mun jira gwamnati ta dauki matakin hanawa ba, mu da kanmu da shugabanninmu da malamai ne ya kamata mu hanzarta daukar matakin hana cusa mutane a cikin mota kamar kifin gwangwani”. Inji shi.