An bukaci ’yan fim su mayar da hankali kan fina-finan bayanai

An bukaci ‘yan fim din Hausa su mayar da hankali kan fina-finan bayanai da ake kira ‘Documentaries’. Malamin Jami’ar Bayero ta Kano Farfesa Uba Abdallah ne ya yi wannan kiran a lokacin taron kaddamar da fim din tarihin rayuwar Dokta Habibu babura wani malami a jami’ar Bayero ta Kano a kwanakin baya.Farfesan wanda ya yi […]

An bukaci ’yan fim su mayar da hankali kan fina-finan bayanai

Dokta Habibu S. Babura wanda aka yi fim din akansaAn bukaci ‘yan fim din Hausa su mayar da hankali kan fina-finan bayanai da ake kira ‘Documentaries’.
Malamin Jami’ar Bayero ta Kano Farfesa Uba Abdallah ne ya yi wannan kiran a lokacin taron kaddamar da fim din tarihin rayuwar Dokta Habibu babura wani malami a jami’ar Bayero ta Kano a kwanakin baya.
Farfesan wanda ya yi sharhi a kan fim din, ya ce: “Dokta Habibu Sani, ya samu nakasa sakamakon hadarin da ya yi lokacin da yake tuka mota daidai mahadar kofar Kabuga ta birnin Kano, a watan Satumba, 1982. Daga nan galibin gabobin jikinsa suka daina aiki.”
Ya ce, finafina (ko documentary da Turanci) bayanai ba su da yawa a kasar nan, “don haka ya kamata ‘yan fim su karkata akalarsu kan fina-finan bayanai, hakan zai koya wa jama’a darasi.” Inji Farfesa Uba.
A lokacin da Dokta babura yake jawabi a lokacin kaddamar da fim a kan rayuwarsa sai ya ce, yana bukatar rayuwarsa ta zame wa sauran masu nakasa da ma masu lafiyar jiki darasi.
Ya ce: “Ya kamata nakasassu su fahimci cewa bara ba ita ce makomarsu ba.”
Alkalin Kotun koli, Mai shari’a dahiru Mustapha daya daga cikin manyan baki ya bukaci gwamnati ta samar da dokokin da za su kyautata rayuwar nakasassu.
Tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Dokta Aliyu Modibo ne babban mai kaddamar da gidauniyar Dokta Habibu babura,  ya bayar da gudunmawar Naira miliyan biyar.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Sunusi Lamido Sunusi, ya ba da Naira dubu dari biyu da hamsin, inda Jami’ar Bayero tare malaman jami’ar suka bayar da Naira miliyan biyu. Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da gudunmawar Naira miliyan biyu, tare da alkawarin yin hadin gwiwa da gidauniyar da za a kafa wajen tallafa wa nakasassu. An tara kimanin Naira miliyan 15 a wajen taron.