An bukaci ’yan fim su rika shirya fim a kan tsaro
Gwamnan Kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ya bukaci ’yan fim su rika shirya fim a kan harkar tsaro don a taimaka wa Gwamnatin Tarayya da ta jihohi wajen magance matsalar tsaron da ta ki ci ta ki cinyewa a Najeriya.Ya yi wannan kiran ne a wajen bikin makon fim na duniya kashi na 10 wanda […]

Gwamnan Kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ya bukaci ’yan fim su rika shirya fim a kan harkar tsaro don a taimaka wa Gwamnatin Tarayya da ta jihohi wajen magance matsalar tsaron da ta ki ci ta ki cinyewa a Najeriya.
Ya yi wannan kiran ne a wajen bikin makon fim na duniya kashi na 10 wanda aka yi a Abuja makon jiya.
Gwamnan wanda Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Alhaji Ahmed dahiru Beli ya wakilta ya ce gwamnati a shirye take ta taimaka wa hukumar tace fina-finai ta jihar da duk wani taimako da take bukata wajen gudanar da ayyukanta cikin jin dadi.
Gwamnan ya roki ’yan fim su rika bin doka da oda ta hanyar kiyaye abubuwan da suka shafi addini da al’ada a cikin fina-finansu.
A nasa jawabin Daraktan Abuja International Film Festibal, Mista Fedielis Duker ya yaba kokarin Gwamnatin Jihar Kano wajen taimaka wa masana’antar shirya fina-finai, musamamn ta bangaren taimaka wa Hukumar Tace Fina-finai ta jihar wajen gudanar da ayyukanta.