An bukaci ’yan Najeriya su girmama dokokin kasa

Wasu shugabannin ’yan Arewacin Najeriya mazauna Jamhuriyar Benin, a karakashin jagorancin Alhaji Muhammad Mouniru Garba Nakura, sun kai ziyarar mubaya’a da neman shawara ga Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin a fadarsa da ke Sasa a birnin Ibadan.Da yake zantawa da ’yan jarida bayan ganawar da suka yi, jagoran al’ummar Arewacin Najeriya da ke […]

An bukaci ’yan Najeriya su girmama dokokin kasa
An bukaci ’yan Najeriya su girmama dokokin kasa

Wasu shugabannin ’yan Arewacin Najeriya mazauna Jamhuriyar Benin, a karakashin jagorancin Alhaji Muhammad Mouniru Garba Nakura, sun kai ziyarar mubaya’a da neman shawara ga Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin a fadarsa da ke Sasa a birnin Ibadan.
Da yake zantawa da ’yan jarida bayan ganawar da suka yi, jagoran al’ummar Arewacin Najeriya da ke zaune a kasar Benin, ya nemi ’yan Najeriya su rika girmama doka da oda, wanda shi ne tubalin ginin kowace kasa da zai daukaka martabarta a duniya. Ya ce: “kasashen duniya da suka ci gaba sun samu zuwa matsayin da suke ciki a yanzu ne saboda girmama dokoki da al’ummarsu suka yi a dalilin kishi da kaunar kasarsu. Muddin muna so mu shiga cikin jerin kasashen da suka ci gaba, to wajibi ne mu rika girmama dokokin kasarmu.”
Ya ce saboda dadewa da ’yan Najeriya suka yi zaune a wannan karamar kasa ta Benin da ke makwabtaka da Najeriya, akwai da yawa daga ’yan Arewacin Najeriya da ake damawa da su cikin harkokin siyasar kasar. Suna tsayawa takarar manyan mukamai a inuwar jam’iyyu domin dokar kasar ta ba su damar yin hakan. Akwai manyan kungiyoyi masu karfi na kabilun Hausawa da Yarbawa da Ibo da shugabanninsu suka yi gamayya domin tafiya da murya daya da gwamnatin kasar take mu’amala da mu wajen kyautata tsaron lafiya da zamantakewa a tsakaninmu da jama’ar gari da harkokin kasuwanci domin bunkasa tattalin arziki.
A jawabin maraba, Alhaji Haruna Maiyasin ya nuna farin ciki da jin dadinsa a game da dangantakar da ke tsakanin kasashen Najeriya da Benin, wanda ya ce ba a taba samun labarin tashin hankali a tsakanin al’ummomin kasashen ba. “Saboda haka ina ba ku shawara, musamman irinku da kuka manta da kasarku bayan Allah ya wadata ku da arzikin da kuka jibge a wasu kasashe da ku dawo gida domin yin amfani da dukiyarku a kauyuka da garuruwanku a matsayin gudunmowar bunkasa tattalin arzikin kasarku Najeriya,” inji shi.