An buqaci gwamnatin Sakkwato ta dakatar da gina shaguna a Kasuwar Kara

Kungiyar masu sayar da dabbobi da suka haxa da rago da shanu da jaki da doki da rakumma a Kasuwar Kara da ke Jihar Sakkwato sun nuna rashin amincewa da shaguna 64 da gwamnati ta shirya ginawa a kasuwar. Shugaban masu sayar da shanu Alhaji Bashiru Bello ya ce wannan aikin ba su gamsu  da […]

An buqaci gwamnatin Sakkwato ta dakatar da gina shaguna a Kasuwar Kara

Gwamnan Aminu TambuwalKungiyar masu sayar da dabbobi da suka haxa da rago da shanu da jaki da doki da rakumma a Kasuwar Kara da ke Jihar Sakkwato sun nuna rashin amincewa da shaguna 64 da gwamnati ta shirya ginawa a kasuwar.

Shugaban masu sayar da shanu Alhaji Bashiru Bello ya ce wannan aikin ba su gamsu  da shi ba kuma ba shi da tsari don da zaran an gina waxannan shaguna za a shigo da wata sana’ar da ba ta da alaka da kasuwancinsu haka na iya haifar musu da wata rigima da za ta zama kalubale a garesu bayan cunkushewar wuri da za a samu, “muna bukatar a duba takardar kokenmu da muka rubuta da kyau don a yi mana adalci,” inji shi.

Ya kara da cewa ba su bukatar a gina shaguna a ba su ko yanka fuloti a raba masu abin da suke son su ja hankalin gwamnati da shi hatsarin da ke cikin gina shagunan a Kasuwar Kara wadda kowa yasan yadda take sarke-sarke a lokacin bukukuwan sallah balle a ce an rage mata faxi a saman hanyar da mutane ke wucewa abu ne da ke bukatar nazari da yi masa gyaran fuska don kaucewa rigima a gaba.

Malam Sirajo Abubakar yabon gwani wanda yake zuwa daga kasar Chadi tare da raguna a kasuwar kuma ya kara nunawa Aminiya suna cikin halin damuwa a kasuwancinsu matukar gwamnati ta amince a gina shagunan kamar yadda aka ce a “yanzu haka an sayar da 61 kan wasu dubu xari bakwai wasu 650 wasu 450.” Ya ce “ko yanzu ya suka kare da masu motoci balle a yi waxannan shaguna don haka yake kira da gwamnatin Sakkwato ta saurari kukansu duk da shi yakan zo ne cin kasuwa ya koma ne.”

Alhaji Buba Gagi shi ne shugaban masu sayar da raguna a kasuwar ya musanta zargin da ‘yan uwansa ke yi na tare da shi aka haxa baki wajen kawo maganar shagunan a kasuwar ya ce gwamnati ce ta ga za ta yi kuma ta bayar da umarnin yanka shaguna kawai. Aminiya ta tuntuvi Kwamishinan Filaye da Gidaje na Jihar Sakkwato Alhaji Bello Guiwa, amma sai jam’in hulxa da jama’a na ma’aikatar ya ce su ba su karbi kowane irin koke daga kowace kungiya ta kasuwar ba kan lamarin. Kuma ya ce za a yi aikin ne don samar da ci gaba da bunkasa kasuwar.