An cafke shi ya kashe mahaifiyarsa da ’ya’yansa

Ya kashe ‘ya’yansa biyu ya jikkata uku ta hanyar saran su da adda da tsakar dare

An cafke shi ya kashe mahaifiyarsa da ’ya’yansa

‘Yan sanda

An cafke wani mutum bayan ya kashe mahaifiyarsa mai shekara 85 da kuma ’ya’yansa biyu.

Mutumin mai shekara 47 ya yi ta sarar tsohuwar tasa da ’ya’yan nasa ne da adda a lokacin da suke barci a Karamar Hukuman Nnewi ta Yamma da ke Jihar Anambra.

Kakarin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Haruna Mohamed, ya tabbatar da aukuwar lamarin yana cewa mutumin ya kuma kakkafta wa wasu ’ya’yansa uku sara da addar kafin a kama shi a ranar Alhamis.

Ya ce yaran da mutumin ya kashe baya ga mahaifiyar tasa sun hada da  mai shekara 9 da kuma mai shekara 2. Wadanda ya raunata kuma sun akwai mai shekara 8,  11 da mai shekara 12.

SP Haruna ya ce an garzaya da yaran da suka samu rauni asibiti yayin da ke bincike domin gano dalilin mutumin na aika-aikan.

An yi garkuwa da ’yar ƙasar waje a Nijar

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo