An cafke Alkalin da ya yi shigar mata yana zana wa budurwarsa jarrabawa

Makonni biyu da suka gabata a daga likafar lauyan zuwa mukamin Alkali.

An cafke Alkalin da ya yi shigar mata yana zana wa budurwarsa jarrabawa

An kama wani sabon alkali mai suna Musa Semwogerere da ya yi shigar mata yana zana wa budurwarsa jarrabawa.

Bayanai sun ce alkalin ya yi sojar gona ne domin zana wa budurwarsa jarrabawa a wata Cibiyar Lauyoyi ta LDC da ke Lira a Kasar Uganda.

Jaridar Congress News ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne bayan makonni biyu da daga likafar Mista Semwogerere zuwa karamin alkali da Hukumar Shari’a ta kasar ta yi.

Mista Semwogerere wanda aka fi sani da Mukisa Anthony ya shiga hannu a ranar Juma’ar da ta gabata yana rubuta wa budurwarsa mai suna Irene jarrabawa.