An cafke babban abokin ango bisa zargin sace kayan lefe a Kano
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne mako daya bayan angon ya tare
A Jihar Kano an cafke wani abokin ango da ake zargi da sace wa amaryar kayan lefen amarya, wadanda kimar su ta kai Naira 500,000.
Lamarin ya faru ne a unguwar Gaida da ke Karamar Hukumar Kumbotso da ke Jihar ta Kano.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne mako daya bayan angon ya tare, shi kuma abokin yana da mukullin gidan a hannu, har ma angon ya nemi ya dawo masa da su, amma ya ki.
Sai dai kuma abokin angon ya yi wa angon gorin cewa shi ma ya kashe masa sama da Naira 400,000 a bikin nasa.
Da ya ke bayani ga manema labarai a Kano, bayan sun cafke wanda ake zargin ranar Alhamis, Kwamandan ’yan sa-kai na unguwar ta Gaida, Shekarau Ali, ya ce binciken da su ka yi ne ya sanya suka gano wanda ake zargi da dan halin.
A cewar kwamandan, wanda ake wa lakabi da Cinnaka, tun da farko angon ne ya kai musu korafin an yi masa sata, inda binciken su ya gano ’yan uwan amaryar ne suka ba wanda a ke zargi da satar mukullin gidan domin ya bai wa angon bayan sun kammala jeren kayan amarya a ciki.
Kwamandan ya ce, “Daga nan ango ya nemi ya ba shi mukullin, amma ya ki, har sai da ya jira sun fita da amaryar, shi ne ya bude gidan ya sace kayan lefe, har da ma wasu kayayyakin abinci.
“Daga nan ne binciken mu ya gano mana cewa shi wannan abokin, shi ne ya ci amana ya tafka wannan sata kuma tuni yana hannunmu,” inji shi.
Ya ce da zarar sun kammala binciken da suke yi a kan shi, za su muka shi ga ’yan sanda don daukar matakin da ya dace a kansa.
Sai dai wanda a ke zargin ya alakanta lamarin da sharrin Shaidan ne, inda ya roki a yafe masa, yana mai alkawarin ba zai sake aikata hakan ba a nan gaba.