An cafke barauniyar dan firamare a Kwara
Kotu ta tsare matar da ake zargi da satar dan makabartar firamare a a gidan gidan yari
Dubun wata mata da ake zargi da sace wani karamin yaro a wata makarantar firamare ta cika a garin Ilori, Jihar Kwara.
An cafke matar mai shekara 29 ne bayan ta yi awon gaba da wani dan firamare a kofar shiga makarantar da ke unguwar Gamno a garin na Ilori.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Magidanci Ya Babbaka Agololinsa 5
- Mahaifiyar Farfesa Ibrahim Malumfashi ta rasu
Ganin ta tsere da yaron ne aka bi ta a guje, inda wani mai babur ya yi nasarar cafko ta tare da yaron ta yi yunkurin sacewa.
“Da aka kalubalance ta sai ta ikirarin cewa ita ce mahaifiyar yaron,” a cewar mai gabatar da kara, Gbenga Ayeni, a lokacin da ake gurfanar da wadda ake zargin a gaban kuliya.
Bayan sauraron karar, alkalin kotun majistaren, Monisola Gbadeyan Kamson, ta ba da umarnin tsare matar a gidan yari, sannan ta dage shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba da muke ciki.