An cafke barawon wayar wuta ta N3m

Ana tuhumar mutumin ne da laifin sata da lalata kayan gwamnati, sai dai ya musanta zargin.

An cafke barawon wayar wuta ta N3m

An gurfanar da wani mutum mai shekaru 32 a wata kotun Majistare da ke Jihar Legas, bisa zargin sa da satar wayar wuta da kudinta ya kai Naira miliyan uku.

Ana tuhumar mutumin ne da laifin sata da lalata kayan gwamnati, sai dai ya musanta zargin.

’Yar sanda mai gabatar da kara Insfekta Adegeshin Famuyiwa ta sanar da kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne da misalin karfe 3:30 na rana a unguwar Majidun akusa da wani gidan mai a titin Ikorodu da ke Legas.

Famuyiwa ta ci gaba da bayyana wa kotun cewa wayar wutar da mutumin ya sace mallakin ma’aikatar wuta ta jihar ce, kuma bayan satar sai da ya lalata wasu daga cikin kayayyakin da ya samu a gurin.

’Yar sandar ta ce wannan aika-aikar ta wanda ake zargin ta saba wa sashi na 287, da na 350 na kundin manyan laifukan jihar na 2015.

Haka kuma ta ce muddin kotun ta same shi da laifin da ake zargin nasa, zai janyo masa daurin shekaru uku da karin wasu shekaru biyu.

Alkalin kotu, Mista A.O Ogbe ya ba da belin wanda ake zargin kan Naira dubu 100, da sharadin gabatar da mutum biyu masu tsaya masa da suka mallaki wadannan kudin.

Haka kuma ya ce dole ne masu tsaya masan su zamo masu alaka ta jini da shi, tare da bayyana fara binciko sahihin adireshinsa.

Daga nan ne kuma ya dage zaman shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Agusta.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara