An cafke barayin dabbobi da dillalinsu a Kano

Dubunsu ta cika bayan sun sace dabbobin jama’a a wurare daban-daban

An cafke barayin dabbobi da dillalinsu a Kano

Wasu barayin dabbobi da suka addabi kauyen Aujawara Alkali da ke Karamar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano sun shiga hannu.

Shi ma ‘barawon zaune’ da ke sayen dabbobin sata daga hannun baraynin dabbobin dubunsa ta cika.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafko ‘barawon zaunen’ ne a yayin da ake gudanar da bincike bayan an kama barayin tumakin.

Barawon awaki

Shi kuma wani barawon awaki a Jihar Legas, dubunsa ta cika ne inda aka kama shi da awaki hudu da ya sato.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Christian Okonofua, ya shaida wa kotu cewa a watan Janairun 2022 ne wanda ake zargin ya shiga wani gida a unguwar Ikorodu ya yi awon gaba da awakin wata mata su hudu.

Ya bayyana wa kotun majistaren cewa kudin awakin da wanda ake zarin ya sace ya kai Naira dubu dari biyu.

Alkalin kotun, Misis T.A. Shotobi, ta bayar da belin wanda ake zargin a kan N100,000 tare da kawo mutum biyu su tsaya mishi, kuma kowannensu zai ajiye N100,000.

Daga nan ta dage zaman zuwa ranar 19 ga watan Mayu.