An cafke buhuna 200 na gurbataccen sukari a Kano

Ma’aikatar muhalli ta Jihar Kano ta gano wani gurbataccen sukari da aka yi kokarin shigar da shi kasuwannin Jihar Kano.Sarkin Tsaftar Kano Alhaji Ja’afaru Gwarzo ne ya tabbatar da gano buhuna dari biyu na gurbataccen sukarin a lokacin da yake nuna wadanda ake zargi da safarar sukarin a tashar jiragen kasa da ke Kano.Alhaji jafaru […]

An cafke buhuna 200 na gurbataccen sukari a Kano

Ma’aikatar muhalli ta Jihar Kano ta gano wani gurbataccen sukari da aka yi kokarin shigar da shi kasuwannin Jihar Kano.
Sarkin Tsaftar Kano Alhaji Ja’afaru Gwarzo ne ya tabbatar da gano buhuna dari biyu na gurbataccen sukarin a lokacin da yake nuna wadanda ake zargi da safarar sukarin a tashar jiragen kasa da ke Kano.
Alhaji jafaru ya ce, ana sayar da gurabataccen sukarin ne ga mutanen da suke yin sana’ar abubuwan sha, musamamn na jika makoshi, danginsu lamurje da tsimi da alawowi, inda ya ce hakan laifi ne da ya saba wa sashe na 14 na dokokin tsaftar muhalli na jihar.
Da yake bayani a kan irin hadarin da ke tattare da  ci ko shan abu gurbatacce kuwa, Sarkin tsaftar ya ce, “ci ko shan kayayyakin abinci wadanda aka gurbata yana janyo hadari ga lafiyar dan adam. Hakan ya sa idan mun ci karo da duk wani abu da zai haddasa cuta ga dan adam mu kan kama mai yinsa tare da hukunta shi. Wannan sukari da muka kama shara ce ta kamfani, wanda suka kawo shi, so suke yi idan dare ya yi su dauka su shiga da shi kasuwa don sayarwa.” Inji sarkin tsaftar.
Da yake bayani, wanda ake zargi da jigilar sukarin, Auwalu Muhammad, ya bayyana cewa, wadansu masu gadin kamfani a Legas ne suka sayar masa da kayan. “Ba shakka wanann sukari shara ce ta kamfanin dangote, mun saye shi ne a wurin wani mutum mai suna Usman Bawa wanda yake fitar da shara ta banagarn kayayaykin da ake yi a kamfanin. Idan mun kawo shi mukan sayar wa masu yin alawa ko masu yin lamurje.” Inji shi.