An cafke dan Najeriya da ya aikata fashi sau 68 a Amurka
’Yan sandan Amurka sun cafke wani dan asalin Najeriya mai shekaru 26 kan aikata fashi da makami sau 68 a yankin Los Angeles.
’Yan sandan Amurka sun cafke wani dan asalin Najeriya mai shekaru 26 kan aikata fashi da makami sau 68 a yankin Los Angeles.
Rundunar ’Yan Sandan Birnin Los Angeles (LAPD), ta cafke matashin, wanda ta yi wa lakabi da ‘Blue Cloth Bandit, kan zargin fashi guda 68 a yankin cikin shekara daya, daga watan Oktoban 2021 zuwa yanzu.
- Gwamnoni da Kwamitin Amintattun APC sun sa labule
- Buhari ya karrama dan sandan da ya ki karbar cin hancin dala dubu 200 a Kano
Kafar yada labaran Amurka ta Fox News ta ce LAPD ta yi masa lakabi da ‘Blue Cloth Bandit’ ne saboda yana ‘amfani da shudin mayafi ya lullube bindigar da yake yin fashi da ita a gidajen da manyan shaguna da sauransu.
“Yakan boye kamanninsa ta hanyar sanya malafa ya tare fuskarsa, sannan ya sanya safar hannu ta roba.
“An yi amfani da wannan motar da aka kama shi da ita a yawancin fashin, kuma an alakanta shi da fashin bisa dalilai da dama.”
Yunkurinsa ‘Blue Cloth Bandit’ na karshe ya auku ne a ranar 23 ga waan Satumba, bayan masu bincike sun fara amfani da kyamarar sanya ido da kuma ba da sammacin bincike.
Bidiyon sanya ido da LAPD ta fitar sun nuna matashin ya je kamar zai yi sayayya a wani shago, amma sai ya zaro bindigarsa da ke lullube da wani shudin kyalle.
An kuma gan shi a cikin bidiyon sanye da shudin safar hannu da hula da ta rufe fuskarsa.
’Yan sanda sun kwace bindigogi da wasu shaidu daga wurin da ya yi yunkurin fashin na karshe.
Tuni dai suka fara tuhumar sa da laifuka 16 na fashi da makami a cikin birnin na LA.
Ana kuma sa ran sashen Sheriff na Los Angeles zai shigar da karin tuhume-tuhume kan wasu fashi da makami da ake ganin sa da aikatawa a gundumar.