An cafke fasto kan damfarar abokin kasuwancinsa
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) ta cafke wani fasto kan damfarar wani mai a harkar hakar ma’adinai a Jihar Kogi.
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) ta cafke wani fasto kan damfarar wani mai a harkar hakar ma’adinai a Jihar Kogi.
Mataimakin Babban Kwamandan NSCDC, Ahmad Ahmad Ghandi, ya ce dubun Fasto Chimezie ta cika ne bayan da ya karbi kudin wani abokin kasuwancina, ya yi gaban kansa da su.
Ghanid ya bayyana cewa, Fastor Chimezie ya karbi Naira miliyan daya ne daga hannun abokin kasuwancin nasa mai suna AbdulBanu da cewa zai zuba masa jari a harkar hakar kwal, amma a babu abin da ya yi na zuba jarin, kuma bai dawo da kudin ba.
Hukumar ta yi holen faston ne a tare da wasu mutum biyu da aka kama kan zargin damfara.
- Yadda ’yan fashi suka kashe mutum 4 a ‘Supermarket’ a Nasarawa
- Hisbah ta kama mota maƙare da kwalaben barasa dubu 24 a Kano
Na farkon an kama shi ne kan damfarar Naira miliyan biyu, da ya karba daga hannun wani mai neman aiki a Hukumar Kula da Lafiyar Teku (NIMASA), sannan ya ba shi takardar daukar aikin hukumar ta bogi.
Na ukun kuma kudin wata mata da suka yi cinikin motarsa ya karba, Naira miliya 1.7, amma daga karshe ya ki ba ta motar kuma ya rike kudin.
Jami’in ya ce bayan samun korafe-korafe da gudanar da bincike ne hukumar ta cafko wadanda ake zargin a wurare daban-daban a jihar.