An cafke fasto kan safarar jarirai

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Akwa Ibom ta cafke wata fasto mai suna Misis Mmayen Odiuotip da wasu mutane biyar bisa zargin sata da kuma cinkin jaririya da aka sace tun shekarar 2018. Rahotanni sun tabbatar da cewa faston mai kimanin shekaru 39 ta amsa laifinta inda ta ce ta sayi jaririyar ne ga wata […]

An cafke fasto kan safarar jarirai

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Akwa Ibom ta cafke wata fasto mai suna Misis Mmayen Odiuotip da wasu mutane biyar bisa zargin sata da kuma cinkin jaririya da aka sace tun shekarar 2018.

Rahotanni sun tabbatar da cewa faston mai kimanin shekaru 39 ta amsa laifinta inda ta ce ta sayi jaririyar ne ga wata ‘yar uwarta mai suna Esther Esin.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Misis Mmayen ta raba wa ‘yan jarida a birnin Uyo ta ce sun kama wadanda ake zargin ne bayan sun samu rahoton sirri.

Sanarwar ta ce , “Mun kama wadanda muke zargin ne bayan mun samu wani kwakkwaran rahoto cewa wata mai suna Rose Bassey Asuquo Ekpenyong ta hada baki da matar da muke zargi suka sayar da wata jaririya ga wata Fasto mai suna Misis Mmayen Etim Out, wacce ita ce shugabar cocin Land of Testimony da ke Oron.

“Daga bisani mun samu nasarar cafke wannan Faston kuma ta amince cewa ‘yar uwarta mai suna Esther Effanga Esin ta sayawa jaririyar.

Da jin haka ne jami’anmu suka bazama suka kuma cika hannu da ita tare da ceto jaririyar,” inji sanarwar ‘yan sandan.

Daga nan kuma ‘yan sandan sun yi kira ga jama’a da su ci gaba da taimakawa da muhimman bayanan da za su tallafa wajen kama masu safarar da satar kananan yara a jihar da ma masu aikata sauran muggan laifuka.

Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 23 A Borno

Fasinjoji sun jikkata yayin da tankar mai ta yi bindiga a Abuja

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu

1.5bn kaɗai aka sanya a asusunmu — Tsohon Kwamishinan Sakkwato