An cafke fataken miyagun kwayoyi a Kano

A kokarinta na yaki da masu sha da fataucin miyagun kwayoyi a Jihar Kano, Rundunar ’Yan sanda a jihar ta cafke akalla mutane 11, wadanda take zargi da laifin safara da fataucin miyagun kwayoyi a jihar. Da yake baje kolin kamammun ga manema labarai, jami’in hudlda da jama’a na ’yan sandan jihar, ASP Magaji Musa […]

An cafke fataken miyagun kwayoyi a Kano
An cafke fataken miyagun kwayoyi a Kano

A kokarinta na yaki da masu sha da fataucin miyagun kwayoyi a Jihar Kano, Rundunar ’Yan sanda a jihar ta cafke akalla mutane 11, wadanda take zargi da laifin safara da fataucin miyagun kwayoyi a jihar.

Da yake baje kolin kamammun ga manema labarai, jami’in hudlda da jama’a na ’yan sandan jihar, ASP Magaji Musa Majiya ya bayyana cewa sun cafke wadanda ake zargin ne a wani samame da jami’ansu suka kai a wani wuri kebantaccen wuri da ke Sabon Gari cikin jihar, inda rundunar tasu ta kama katon 32 shake da kwayoyi masu sa maye da ledoji 30 kunshe da tabar wiwi. Haka kuma akwai wasu katon 43 na kwayoyin Tramol.
Majiya ya kara da cewa binciken ’yan sanda ya gano cewa wadanda ke safarar miyagun kwayoyin sun hada da Mista Obinna Nwosu da Ibe Ugoh da Bitrus Nuwagu, wadanda dukanninsu ’yan asalin Jihar Imo ne.
“Baya ga wadanda aka kama ’yan asalin Jihar Imo, akwai wani kuma wanda dan asalin Jihar Ebonyi ne, wanda kuma ya zo Kano shekaru biyu da suka wuce da niyyar zai yi noma; inda kuma a karshe ya bige da safarar miyagun kwayoyi.” Inji Majiya
Har ila yau, ya bayyana cewa rundunarsu ta kama wani babur mai kafa uku, wanda aka yi watsi da shi a kan titin Obasanjo dauke da buhuna 25 na tabar wiwi kwanaki kadan bayan kama masu safarar miyagun kwayoyin.
Jami’in ya jaddada alwashin cewa rundunar ’yan sanda ta daura damara wajen yaki da masu sha da fataucin miyagun kwayoyi.