An cafke kwandasta kan zargin fyade a cikin mota

’Yan sanda sun tsare wani kwandasta kan zargin yi wa wata ’yar shekara 15 fyade a cikin mota.

An cafke kwandasta kan zargin fyade a cikin mota

Fyade

’Yan sanda sun tsare wani kwandasta kan zargin yi wa wata ’yar shekara 15 fyade a cikin mota.

Kakakin ’yan sandan jihar Edo, SP Chidi Nwabuzor, ya ce mahaifin yarinyar ne ya kawo kara cewa yaron motar mai shekara 28, ya zakke wa ’yarsa da karfin tuwo a cikin mota.

Ya ce mahaifin yarinyar ya bayyana musu cewa ’yar tasa tana cikin tallar gyada ne wanda ake zargin ya kira ta da sunan cewa zai saya.

Amma, “Da ta kawo sai ya cacume ta da karfin tsiya ya jefa a cikin mota ya keta budurcinta, daga baya ’yan sanda suka je suka kamo shi,” in ji jami’in.

A cewarsa, yaron motar ya amsa laifinsa da ake zargin sa da aikatawa, ita kuma yarinyar an kai ta asibiti domin duba lafiyarta.

Ya ce lamarin ya faru ne a kan titin Ivue-Irrua da ke Karamar Hukumar Esan ta Kudu ta jihar, a ranar 13 ga watan nan na Satumba.

‘Sharri aka yi min’

Sai dai a yayin da ’yan jarida ke masa tambayoyi, wanda ake zsargin, ya bayyana musu cewa kazafi ake masa, kuma hatta yarinyar sai da ta ba da shaida cewa bai yi mata fyade ba.

Ya ce abin da ya faru shi ne: “Muna ta fiya ne a hanyar Agbor zuwa Okpella, amma sai muka makale a Uromi na tsawon kwanaki saboda rashin kyan hanya.

“Ran nan sai muka kira wata mai tallar gyada, na sayi na N100, shi ne abokina ya ce ya ga yarinyar na da natsuwa, da mai dai in aure ta; cikin wasa na ce, to bari idan muka dawo zan je mu yi magana da iyayenta, shi ke nan ta yi tafiyarta.

“Bayan kusan awa uku, ina kwance a cikin mota sai ga ta ta dawo wajena, tana tambaya ta shin da gaske nake maganar auren ta? Muna zaune a cikin motar sai ga wani yaro ya leko, ya fara zargi na da yi mata fyade.

“Na ce masa ko kadan, ita ma yarinyar ta ce masa ban yi mata fyade ba, sai duk suka tafi.

“Bayan dan lokaci sai wasu matasa kuma suka zo suna zargin cewa na yi mata fyade, shi ne aka kawo ni ofishin ’yan sanda, amma ni ban aikata ba.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna