An cafke likitan bogi a Asibitin Malam Aminu Kano

A karshen makon jiya ne jami’an tsaron Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano suka kama wani mutum da ke gabatar da kansa a matsayin likitan aisbitin inda yake karbar kudi daga jama’a da niyyar zai samar musu da aiki a asibitin. Mutumin wanda tsohon ma’aikacin asibitin ne mai suna Salisu Abdullahi yana bayyana kansa da […]

An cafke likitan bogi a Asibitin Malam Aminu Kano
An cafke likitan bogi a Asibitin Malam Aminu Kano

A karshen makon jiya ne jami’an tsaron Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano suka kama wani mutum da ke gabatar da kansa a matsayin likitan aisbitin inda yake karbar kudi daga jama’a da niyyar zai samar musu da aiki a asibitin.

Mutumin wanda tsohon ma’aikacin asibitin ne mai suna Salisu Abdullahi yana bayyana kansa da Dokta Salisu Mijinyawa kuma ya shiga hannun ne lokacin da yake karbar kudi daga hannun wani mai neman aiki mai suna Auwalu Shehu.
Malam Ukashatu Musa Panshekara, shugaban jami’an tsaron asibitin ya shaida wa Aminiya cewa “Mai neman aikin ne ya sanar da mu halin da ake ciki bayan ya fara zargin akwai rashin gaskiya a cikin lamarin, wato a yayin da suka yin yarjejeniyar zai ba likitan bogin Naira dubu 10 da niyyar zai cika masa sauran Naira dubu 30 bayan an samu aikin kamar yadda suka yi alkawarin zai biya shi Naira dubu 40 idan ya samar masa aikin. A lokacin da zai karbi kudin ne muka kama shi,” inji shi.
Yayin da yake musanta laifin da ake zarginsa, likitan bogin ya ce shi bai taba gabatar da kansa a matsayin likita ba haka bai taba karbar kudi daga hannun kowa da niyyar samar masa aiki ba. “Ban taba bayyana kaina a matsayin likita ba. Ni dai ina taimakon
mutane ina samar musu aiki ne kawai, ba na kuma cewa sai sun ba ni kudi. Sai dai ina karba daga wanda ya ga dama ya ba ni don nuna jin dadin abin da na yi masa,” inji shi
Shugaban jami’an tsaron ya bayyana wa Aminiya cewa za su mika wanda ake zargin ga ofishin ’yan sanda na Unguwa Uku da ke Kano.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi