An cafke likitoci 2 kan satar ƙodar mara lafiya a Jos

An gano cewa Noah Kekere da ake zargi da sace ƙodar mara lafiya, likitan bogi ne

An cafke likitoci 2 kan satar ƙodar mara lafiya a Jos

’Yan sanda sun cafke wasu ƙarin likitoci biyu kan zargin haɗa baki da sace ƙodar wani mara lafiya a Jos, babban birnin Jihar Filato.

Ana zargin likitocin biyu ne da haɗa baki da kuma aiki tare da wani Dokta Noah Kekere na Asibitin Murna da ke garin Jos, wajen cire ƙodar wani mara lafiya mai suna Kehinde Kamal.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya shaida wa ’yan jarida cewa ana gudanar da bincike a kan waɗanda ake zargin.

A cewarsa, Kwamishinan ’yan sandan jihar ya kafa kwamitin ƙwararrun likitoci domin gudanar da bincike su gano gaskiyar zargin cire ƙodar mara lafiyan.

A cewar kakakin ’yan sandan, runduna ta kuma gano cewa Noah Kekere ba likita ba ne, kamar yadda yake gabatar da kansa.

’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

Za a ɗauke wutar lantarki na tsawon mako 2 a Abuja

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota