An cafke limamin da yake ikirarin Annabta da baiwar tayar da matattu
Wani limamin mabiya addinin Kirista, Fasto Onyebuchi Okocha da ya yi ikirarin Annabta da da’awar baiwar tayar da matattu ya shiga hannu a Jihar Anambra. Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Anambra, CSP Haruna Muhammad ne ya inganta rahoton wanda a cewarsa za a gurfanar da wanda ake zargi da zarar bincike ya […]
Wani limamin mabiya addinin Kirista, Fasto Onyebuchi Okocha da ya yi ikirarin Annabta da da’awar baiwar tayar da matattu ya shiga hannu a Jihar Anambra.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Anambra, CSP Haruna Muhammad ne ya inganta rahoton wanda a cewarsa za a gurfanar da wanda ake zargi da zarar bincike ya kammala.
- Hukuncin kisa zai tabbata a kan masu satar mutane — Lalong
- Gwamnatin Kaduna ta sanar da ranar sake bude makarantun sakandiren jihar
- An rushe gidan wadanda ake zargi da satar mutane a Kuros Riba
CSP Haruna ya ce mutumin da ake zargi ya shiga hannu ne tun a ranar Laraba, 27 ga watan Janairun 2021.
Mutumin da ake zargi mai inkiyar ‘Onyeze Jesus’ ya yi ikirarin cewa shi Annabi ne cikin wani sako na hoton bidiyo da ya wallafa wanda bayyana cewa zai tayar da gawar mutum bakwai da aka killace a dakin ajiyar gawa na wani asibiti.
Onyebuchi wanda a yanzu ya shahara, shi ne ya kafa Cocin Children of Light Anointing Ministries a yankin Nkpoe na Karamar Hukumar Idemili ta Arewa a Jihar Anambra.
Tun gabanin shigarsa hannu, Gwamnatin Jihar cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a 25 ga watan Janairu, ta gargadi limamin kan ayyukan da ya ke aikatawa wanda a cewarta laifi ne da ya saba wa koyarwar kowane addini.
Gwamnatin ta yi wannan gargadi ne ta bakin Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da kan Al’umma, Mista C Don Adinuba, lamarin da ta ce babban laifi ne da yake bata tarbiya.
Kazalika, Ma’aikatar Lafiya ta Jihar, a sanarwar da ta fitar a ranar Laraba ta gargadi asibitoci a jihar da masu ajiye gawarwaki a kan kada su sake su bai wa mutumin damar shiga wurin da suke ajiye gawarwaki da sunan tayar da matattu da siddabaru.
Mutane da dama sun bayyana damuwarsu a kafafen sada zumunta kan hoton bidiyon da Onyeze Jesus ya fitar na wasu gardawa tsirara a cikin rafi yana watsa musu kudade da sunan wai za su yi arziki.
Aminiya ta samu cewa mutumin wanda da yake wannan da’awa mai kimanin shekaru 32, ya taba kasancewa karen mota kuma bai kammala karatunsa na Firamare ba.