An cafke mafarauta kan garkuwa da mutane a Adamawa
’Yan sanda sun cafke mafarautan da abokan cin mushensu ne a kauyukan Pariya Daware da kuma Girei inda suka hana mazauna kauyukan sakat
Wasu mafarauta sun shiga hannu kan zargin yin garkuwa da mutane a kauyukan kananan hukumomin Girei da Fufure na Jihar Adamawa.
’Yan sanda sun cafke mafarautan da abokan cin mushensu ne a kauyukan Pariya Daware da kuma Girei inda suka hana mazauna kauyukan sakat.
- ’Yan bindiga sun sace mutum 50 a Sakkwato
- Cikakken tsaro muke bukata —’Yan Najeriya ga gwamnati
- Mahara sun kashe mutum 11, sun kone ilahirin kauye a Binuwai
Kakakin ’yan sandan Jihar Adawamawa, SP Sulaan Nguroje, ya ce, “Bincike ya gano wadanda ake zargin sun ci amanar mutanen yankin da suka aminta da su domin su kare rayuka da dukiyoyinsu.
“Maimakon haka sai suka rika amfani da damar wajen yi wa masu garkuwa da mutane a yankin safarar kayan abinci da sauran kayan masarufi.”
SP Nguroje ya ce an kwace bindiga kirar Pistol da babur da sauran abubuwa a hannun mafarutan da dubunsu ta cika.
Ya ci gaba da cewa mafarautan da aka kama shekarunsu 28 ne zuwa 40.