An cafke matar da ke damfara da sunan Aisha Buhari

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana cewa ta kama wata da ke yin sojan-gona a mastayin matar shugaban kasar, Hajiya Aisha Buhari tana damfarar al’umma. Wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Anjuguri Manzah ya shaida wa manema labarai, ta bayyana cewa an kama matar mai suna Aisha Muhammed Bello ‘yar asalin Jihar […]

An cafke matar da ke damfara da sunan Aisha Buhari
An cafke matar da ke damfara da sunan Aisha Buhari

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana cewa ta kama wata da ke yin sojan-gona a mastayin matar shugaban kasar, Hajiya Aisha Buhari tana damfarar al’umma.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Anjuguri Manzah ya shaida wa manema labarai, ta bayyana cewa an kama matar mai suna Aisha Muhammed Bello ‘yar asalin Jihar Filato mai kimanin shekaru 37.

Sanarwar ta ambato Kwamishinan ‘Yan Sanda na Abuja, Mista Sadik Abubakar Bello na cewa “rundunar ta iza keyar wata mata mai suna Aisha Muhammed Bello da ke damfarar mutane da suna matar shugaban kasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari.

“Matar, mai ‘ya’ya hudu daga Jihar Filato na yin amfani da sunan mai dakin shugaban kasa domin neman kwangila da kuma tallafin kudi daga mutane daban-daban, musamman shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnati.

Sanarwar ta kara da cewa jami’an ‘yan sandan sun kama matar ne a ranar 10 ga Watan Janairu bayan sun samu rahotannin da ke cewa ta nemi taimakon kudi a wurin wani jami’in hukumar Fadama III Project.

“Bayan an kama ta ne kuma aka gano wata wayar tarho mai dauke da layin da aka yi wa rijista da sunan Aisha Buhari, matar shugaban kasa. Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran mutanen da ta damfara, sannan da zarar an kammala binciken, za a gurfanar da ita a gaban kotu don fusknatar hukuncin da ya dace da ita,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.