An cafke matasa biyu kan zargin yi wa ’yar shekara 12 fyade a Ribas
Daya daga cikinsu ya cika bujensa da iska.
Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sandan Jihar Ribas, ya cafke wasu matasa biyu bisa zargin yi wa wata yarinya mai shekara 12 fyade a Karamar Hukumar Akpor da ke Jihar.
Rahotanni sun bayyana cewar matasan wadanda su uku ake zargi da aikata laifin, guda biyu daga cikinsu sun shiga hannun jami’an tsaro a ranar Litinin, yayin da na daya ya cika bujensa da iska.
- Buhari ya nada Bello Koko a matsayin shugaban hukumar NPA
- Matan Kannywood sun fasa maka Sarkin Waka a kotu
An mayar da matasan sashen kare hakkin dan adam na rundunar binciken kwakkwafi a ranar Talata don ci gaba da bincike.
Mahaifin yarinyar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewar matasan guda uku, sun sace ’yarsa a watan Nuwambar 2021, yayin da ta fita zubar da shara, inda suka kai ta wani kango wanda a nan ne suka rike ta har na tsawon awa uku suna keta mata haddi.
Mahaifin nata, ya bayyana cewar an yi nasarar cafke matasan bayan binciken wata biyu da jami’an tsaro suka gudanar karkashin umarnin Kwamishinan ‘yan sandan jihar.
Kazalika, mahaifin yarinyar ya ce binciken likitoci ya bayyana yadda ake ji mata raunuka daban-daban.
Rundunar ‘yan sandan jihar, ta tabbatar da cafke matasan biyu wanda yanzu haka suna komarta inda ake gudanar da bincike kafin mika su gaban kuliya.