An cafke matashi yana yi wa mahaukaciya fyade a Suleja

Matashin ya roke da a yi masa afuwa.

An cafke matashi yana yi wa mahaukaciya fyade a Suleja

Dubun wani matashi mai shekara 21 ta cika, bayan da aka kama shi yana lalata da wata mata mai tabin hankali a Angwan Gwari Kwamba da ke Karamar Hukumar Suleja, a Jihar Neja.

Kafin ’yan sanda su yi awon gaba da wanda ake zargin, an gan shi cikin wani bidiyo da wani John Daniel ya bai wa wakilinmu, inda matashin yan kokarin yi wa mahaukaciyar fyade, kafin daga bisani ta yi kururuwar neman dauki daga mutane.

Matashin, wanda aka same shi da kullin tabar wiwi , ya dora alhakin faruwar lamarin ga shaye-shaye da kuma tsinuwa da mutanen kauyensu suka masa.

Sai dai ya ce yanayin da ya ga mahaukaciyar babu kaya a jikinta ne ya ja hankalinsa.

Ya ce, “Ba don jami’an tsaro ba, da watakila na yi lalata da ita; ban san abin da ya zo mini ba, don Allah yafe ni, shekaruna  21 kacal.

“Akwai abubuwa da yawa a raina, matsalolina na da yawan gaske, ba ni da wanda zai taimake ni.”

Doka da ta tanadi daurin rai-da-rai ga wanda aka same shi da laifi yin fyade ga mace mai hankali, wadda ba za ta iya amincewa wajen saduwa da ita ba.